Kano: Ganduje Ya Sanya Labule da 'Yan Majalisar NNPP, an Fara Batun Komawa APC
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gana da wasu mambobin jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano
- Ganduje ya sanya labulen ne da wasu ƴan majalisar NNPP waɗanda ke takun saƙa da jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso
- A cewar hadimin Ganduje, ganawar ta su na daga cikin shirin sauya sheƙar da suke yi daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanya labule wasu fitattun ƴan majalisar jam’iyyar NNPP daga Jihar Kano.
Sanya labulen da Ganduje ya yi da ƴan majalisar ya ƙara ingiza jita-jita game da sauya sheƙarsu zuwa jam'iyyar APC kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Asali: Facebook
Hadimin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Aminu Dahiru Ahmad, ya sanya hoton ganawar ƴan siyasan a shafinsa na Facebook da yammacin ranar Talata, 15 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanne jiga-jigan NNPP Ganduje ya gana da su?
Cikin waɗanda suka halarci taron akwai Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa.
Sannan akwai Rt. Hon. Kabiru Alhassan Rurum, mai wakiltar mazaɓar Rano/Kibiya/Bunkure a majalisar wakilan tarayya.
Sauran sun haɗa da Hon. Aliyu Sani Madaki, mai wakiltar mazaɓar Dala, da tsohon ɗan majalisa, Hon. Badamasi Ayuba.
A cewarsa, taron yana cikin shirin da ƴan siyasar ke yi na ficewa daga jam’iyyar NNPP mai mulki a Kano zuwa APC.
"Sanin kowa ne a kwanakin baya an jiyo waɗannan jiga-jigan sun bayyana irin rashin adalcin da jagoran NNPP da Kwankwasiyya Dr Rabi’u Kwankwasiyya ya ke musu."
"Wannan dalili ya sa su ke ƙoƙarin ficewa daga jam'iyyar zuwa jam'iyyar APC mai albarka."
- Aminu Dahiru Ahmad

Asali: Facebook
Akalar siyasar Kano na iya sauyawa kafin 2027
Masu fashin baƙin siyasa na ganin cewa shirinsu na sauya sheƙa zuwa APC zai iya sauya akalar siyasa a jihar Kano, wadda ke ɗaya daga cikin jihohin da ke da tasiri sosai a harkokin zaɓe.
A shekarar 2023, jam’iyyar NNPP ta zama mafi ƙarfi a siyasa jihar Kano ƙarƙashin tafiyar Kwankwasiyya.
Sai dai a yanzu tana fama da rikice-rikicen cikin gida waɗanda ke ci gaba da ƙaruwa, inda manyan mambobinta ke zargin shugabannin Kwankwasiyya da nuna musu son kai da wariya.
Jam’iyyar NNPP ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba kan ganawar da ƴan majalisar suka yi da Abdullahi Umar Ganduje.
Ganduje ya faɗi shirin APC kan wasu jihohi
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirin da suke da shi na ƙara faɗaɗa ikon da jam'iyyar ke da shi.
Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar APC na da shirin ƙwato wasu jihohi daga hannun jam'iyyun adawa.
A cewar Ganduje, APC ta shirya ƙara yawan jihohin da take da su a halin yanzu domin ƙara samun rinjaye a faɗin ƙasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng