Ganduje Ya ce Kwankwaso zai Bar NNPP, Ya Dawo Jam'iyyar APC

Ganduje Ya ce Kwankwaso zai Bar NNPP, Ya Dawo Jam'iyyar APC

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa NNPP ta mutu kuma za a birne ta nan ba da jimawa ba
  • Ganduje ya ce tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa APC bayan ya rasa goyon bayan ‘ya’yansa a NNPP
  • Ya kuma ce gamayyar da ake kokarin yi don kalubalantar Bola Tinubu a 2027 za ta ruguje, kuma da yawa daga cikin ‘yan adawar za su dawo APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta mutu, kuma za a birne ta nan kusa.

Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin wata ziyarar girmamawa da kungiyar masu mara wa Shugaba Tinubu baya suka kai sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: APC ta bukaci Ganduje ya taya ta kwato Kawu Sumaila daga NNPP

Ganduje
Gandjue ya ce Kwankwaso zai koma APC. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje|Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa ya ce APC na da buɗaɗɗiyar zuciya wajen karɓar tsofaffin jiga-jigan ‘yan siyasa ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso idan har ya yanke shawarar dawowa gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Jam’iyyar NNPP ta mutu” — Ganduje

Ganduje ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta rasa duk wani karfi da tasiri da take da shi, musamman a jihar Kano, inda ya ce ‘yan jam’iyyar da dama sun bar ta.

Ya ce:

“NNPP ta mutu. Kuma ba da jimawa ba za a birne ta. Amma abin da ya rage shi ne a hako kabari, kuma har an fara hakan. Muna jiran a kammala shiryawa ne kawai.”

Ya ce a yanzu ma jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa (Kwankwaso) ya fara yunkurin dawowa APC saboda ya fahimci cewa ya rasa komai a jam’iyyar da ya tallata.

Kwankwaso Zai iya komawa APC inji Ganduje

Kara karanta wannan

'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027

Ganduje ya ce kofa a buɗe take ga duk wanda ya shirya dawowa APC, yana mai cewa Kwankwaso zai samu tarba mai kyau idan ya dawo gida.

“Za mu karɓe shi idan ya dawo, domin gida zai dawo,”

- Abdullahi Ganduje

Ya kara da cewa APC ta na ci gaba da karɓar fitattun ‘yan siyasa daga sassa daban-daban, wanda hakan ke ƙara ƙarfafa jam’iyyar a fadin ƙasa.

Ganduje: 'Gamayyar adawa za ta rushe'

Ganduje ya kuma ce gamayyar da wasu ‘yan siyasa ke ƙoƙarin yi domin kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 za ta rushe kafin lokaci.

Leadership ta wallafa cewa Ganduje ya ce:

“Wannan gamayya da ake ta surutai a kai, za ta tarwatse kafin ta gama haduwa. Yawancin su za su dawo cikin APC, domin sun san cewa nan ne gida.”

Ganduje ya kammala da jaddada cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da jan ragamar mulki a Najeriya saboda ingantattun manufofi da kuma salon shugabancin Tinubu.

Kara karanta wannan

Atiku: Gwamna ya fadi dalilin Gwamnonin PDP na watsi da kawancen jam'iyyu

Ganduje
Ganduje ya ce 'yan adawa masu shirin hadaka za su wargaje. Hoto: Abdullahi Ganduje
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC na zawarcin Kawu Sumaila

A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar APC a Kano ta Kudu sun fara zawarcin Sanata Kawu Sumaila.

Shugabannin sun bayyana cewa dama Kawu Sumaila dan APC ne kafin ya sauya sheka saboda haka gida zai dawo.

Sun bukaci Abdullaji Ganduje da Sanata Barau Jibrin da su taimaka wajen jawo hankalin Kawu Sumaila zuwa jam'iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel