2027: Sanatan APC Ya Tabo Batun Tazarcen Gwamna Namadi, Ya ba 'Yan Siyasa Shawara

2027: Sanatan APC Ya Tabo Batun Tazarcen Gwamna Namadi, Ya ba 'Yan Siyasa Shawara

  • Sanata Abdul Hamid Malamadori ya yaba da irin ayyukan ci gaba da Gwamna Umar Namadi yake yi a jihar Jigawa
  • Abdul Hamid wanda ke wakiltar Jigawa ta Arewa maso Gabas a majalisar dattawa ya nuna goyon bayansa kan tazarcen gwamnan
  • Ya shawarci ƴan siyasa masu son neman kujerar gwamna da su haƙura domin sai Mai girma Namadi ya yi wa'adin mulki sau biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Jigawa - Shugaban kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƴan sanda, Sanata Abdul Hamid Malamadori, ya yi magana kan batun tazarcen gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi a 2027.

Sanata Abdul Hamid ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Gwamna Umar Namadi zai samu wa’adin mulki na biyu cikin sauƙi, duk da yawan masu neman kujerar.

Gwamna Umar Namadi
Gwamna Namadi ya samu goyon baya kan zaben 2027 Hoto: @uanamadi
Asali: Facebook

Sanata Abdul Hamid Malamadori, wanda ke wakiltar Jigawa ta Arewa Maso Gabas a majalisar dattawa, ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya saba da jam'iyyarsa, ya nuna goyon baya ga tazarcen Tinubu a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Namadi ya samu goyon baya

Ya yi magana ne yayin shirin tattaunawa tsakanin jama’a da gwamnati da aka gudanar a ƙaramar hukumar Birniwa ta jihar.

“Babu gurbin kujerar gwamna a Jigawa a babban zaɓen 2027 mai zuwa, domin Namadi tuni ya riga ya same ta."

- Sanata Abdul Hamid Malamadori

A cewar sanatan, muhimman ayyukan da Gwamna Umar Namadi ya gudanar sun isa su ba shi damar yin wa’adi na biyu.

"Ayyukan ci gaban al'umma, ilmi da sauye-sauye a fannin tattalin arziƙi da gwamnan ya kawo sun tabbatar da wa’adinsa na biyu a shekarar 2027."

- Sanata Abdul Hamid Malamadori

Wace shawara aka ba ƴan siyasa a Jigawa?

Sanatan ya shawarci dukkan waɗanda ke mafarkin hawa kujerar gwamna a Jigawa, ko dai daga cikin APC ko daga wasu jam’iyyun siyasa, da su ajiye burinsu domin babu gurbi a gidan gwamnatin a zaɓen 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane kusan 50, gwamnan Plateau ya fito ya nemi alfarma

Sanatan ya bayyana cewa gwamnan ya cancanci a sake zaɓensa domin ya kammala burinsa na gina jihar Jigawa wacce za ta yi suna a wajen noman zamani.

Gwamna Umar Namadi
Sanata Abdul Hamid ya goyi bayan tazarcen Gwamna Namadi Hoto: @uanamadi
Asali: Twitter
“Bari na ba da shawara ga dukkan ƴan siyasa a wannan jiha da su marawa Gwamna Namadi baya tare da goyon bayan takararsa ta wa’adi na biyu, kuma su daina mafarkin karɓar kujerarsa."
“Gwamna Umar Namadi yana yin aiki sosai, saboda haka babu buƙatar wani ya yi tunanin kalubalantarsa a zaɓen 2027, domin hakan zai zama ɓata lokaci ne kawai."
“Gwamna Namadi ya cancanci yin wa’adi na biyu a shekarar 2027 saboda nagartattun ayyukan da yake yi."

- Sanata Abdul Hamid Malamadori

Gwamnatin Jigawa ta raba babura

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umar Namadi, ta raba babura domin farfaɗo da harkar noma.

Gwamnatin ta raba babura guda 300 ga ma'aikatan wayar da kan manoma domin bunƙasa harkar ayyukan noma a faɗin jihar.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa an raba baburan bisa tsarin rance wanda babu kuɗin ruwa a cikinsa, sannan za a biya cikin watanni 60.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng