'Mun ba Ka Zaɓi': PDP Ta Taso Gwamna a Gaba, Ta Buƙaci Tinubu Ya Sanya Dokar Ta Ɓaci
- Jam’iyyar PDP a Ondo ta yi barazanar neman dokar ta-baci idan Gwamna Aiyedatiwa ya kasa magance matsalar tsaro mai tsanani
- PDP ta zargi gwamnati da yi shiru a matsalar tsaro, tana mai cewa ana kashe manoma da sace mutane ba tare da daukar mataki ba
- Kakakinta, Leye Igbagbo ya ce gwamnati na nuna kamar babu wata matsala, duk da cewa rayukan mutane na salwanta a kowane lungu na jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Jam’iyyar PDP reshen Ondo ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta-ɓaci a jihar.
Jam'iyyar ta ce hakan ya zama dole saboda Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya gaza magance rashin tsaro.

Asali: Twitter
Daraktan yada labaran PDP a jihar, Leye Igbagbo ya ce Aiyedatiwa ya kasa shawo kan kashe-kashen manoma da sace mutane, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokar ta-ɓaci: Gwamna ya soki ƴan adawa
Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Hyacinth Alia ya yi fatali da masu kiran gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta ɓaci a jihar Benue ganin irin halin da ake ciki.
Alia ya ce babu wani dalili da ya kai a ayyana dokar ta ɓaci, ya na mai cewa wasu ƴan siyasa ne ke kokarin fakewa da hakan don cimma burinsu.
Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, lamarim da ya ta da ƙura a kasar.
PDP ta yi barazana ga gwamnan Ondo
PDP a jihar ta ce gwamnatin na mayar da hankali kan abubuwan banza, maimakon ta fuskanci matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a fadin jihar.
Sanarwar mai taken “Ka Zama Mai Hankali a Ayyukanka,” ta bayyana yadda mutane ke rayuwa cikin fargaba saboda karancin tsaro da ya addabi jihar.

Asali: Facebook
PDP ta soki gwamna kan matsalar tsaro
PDP ta ce ta damu da yadda ake yawan kashe bayin Allah da ba su yi komai ba sai kokarin neman abinci ta hanyar halal a Ondo.
Igbagbo ya ce:
“Jam’iyyar ba za ta iya fahimtar yadda ‘yan ta’adda ke aiki ba tare da wani kalubale ba a jihar da gwamnati ke nan daram.
“Abin takaici ne cewa a kasa da wata guda, sama da mutane hamsin aka kashe a wurare daban-daban, kuma ba a kama kowa ba."
Jam’iyyar PDP ta tambaya ko gwamnati har yanzu tana aiki, ganin yadda ake kashe-kashe marasa dalili ba tare da wata matsaya daga gwamnati ba.
PDP reshen jihar ta soki yadda ake tafiyar da tsaro, ta bukaci Aiyedatiwa ya daina siyasantar da rayukan jama’ar da ya rantse zai kare, cewar The Guardian.
Kungiya ta buƙaci sanya dokar ta-ɓaci a Zamfara
Kun ji cewa wata ƙungiya a Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro.

Kara karanta wannan
Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa
Kungiyar CAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu.
NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng