'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dage cewa dole ne a hada kai don a karbe mulki daga Bola Tinubu a 2027
  • Gwamnonin PDP guda 11 sun nesanta kansu daga hadin gwiwa da Atiku ke kokarin kafawa tare da sauran shugabannin hamayya.
  • Atiku ya ce wannan yunkuri mallakin jama’a ne, kuma yana da karfin da zai ci gaba har sai gwamnonin sun fahimta, su hada kai
  • Gwamnonin PDP sun bukaci yankin Kudu maso Gabas ya gabatar da shirin nadin sakataren jam’iyya tare da fuskantar matsalolin tsaro

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya dage cewa kafa kawance ce kadai hanyar da za ta tumbuke Bola Tinubu a zaben 2027.

Atiku Abubakar ya soki matsayar gwamnoni 11 na PDP da suka nesanta jam’iyyar daga hadin gwiwar da tsohon mataimakin shugaban kasar ke jagoranta.

Kara karanta wannan

"Karshen PDP ya zo," George ya hango abin da zai faru idan aka ba Atiku takara a 2027

Atiku ya saba da matakin gwamnonin PDP kan hadaka
Atiku Abubakar ya shawarci gwamnonin PDP kan haɗaka da tuge Tinubu a 2027. Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Yayin da yake magana da jaridar Punch ta bakin hadiminsa, Paul Ibe, Atiku ya ce wannan ya nuna bukatar karin tuntubar juna a tsakanin ‘yan jam’iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan taron su da aka yi a Ibadan ranar Litinin, Gwamnonin PDP karkashin Bala Mohammed sun bayyana cewa ba za su shiga kowace kawance ko hadaka ba.

Sanarwar ta tayar da muhawara, inda bangarori daban-daban ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yiwuwar nasarar kawancen.

Amma yayin karanta sanarwar gwamnoni 11, Gwamnan Bauchi ya ce maimakon shiga kawance, PDP na maraba da duk wanda ke son hada kai da su.

Ya ce:

“Duba da rade-radin hada jam’iyyu ko kungiyoyi, mun yanke shawarar cewa PDP ba za ta shiga kowace kawance ko haɗaka ba.”
Gwamnonin PDP sun fadi matsayarsu kan shirin haɗaka
Matakin gwamnonin PDP kan shirin hadaka ya tayar da kura. Hoto: @seyimakinde.
Asali: Twitter

Martanin Atiku kan matsayar gwamnonin PDP

A martaninsa, Atiku ya bayyana gwamnoni a matsayin manyan jagororin PDP, amma ya ce wannan yunkuri ya riga ya zama mallakin jama’a.

Kara karanta wannan

'Fubara zai dawo kujerarsa nan kusa,' Abokin Wike ya yi wa 'yan Rivers albishir

Ya ce:

“Gwamnoni manyan jiga-jigan kowace jam’iyya ce, ciki har da PDP, amma kowa yana da muhimmanci, har da ‘yan Najeriya na kasa.
“Tun farko, mun gudanar da bincike na ciki da ya nuna cewa wannan ce hanyar da ya kamata mu bi don ceto Najeriya daga hannun masu cin zarafi.
“Don haka ba bazata ba ce muke bin wannan hanya. Ina ganin lokaci ne ke tafiya, kuma nan gaba za a samu daidaituwa da fahimta.”
“Yunkurin ba ya rage darajar gwamnoni, domin su ma suna da muhimmanci, amma ‘yan Najeriya sun fi komai mahimmanci a wannan lokaci.”

An zargi gwamnonin PDP saboda kin haɗaka

Kun ji cewa dan PDP, Dele Momodu ya zargi wasu gwamnonin PDP da kin hadin gwiwa da sauran jam’iyyu, ya ce suna iya boyewa su marawa APC baya.

Dele Momodu ya ce babu wata jam’iyyar adawa da za ta iya kada Tinubu idan ba su hade suka yi aiki tare kamar yadda APC ta yi a shekarar 2015 ba.

Hakan ya biyo bayan matsayar gwamnonin PDP cewa babu wani shiri na haɗaka da suke yi da jam'iyyun adawa game da zaben 2027 da ake tunkara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng