Rigima Ta Ɓarke a Ofishin Jam'iyyar APC, An Tarwatsa Taron Naɗa Sabon Ɗan Takara
- Taron jam’iyyar APC a Legas, ya rikide zuwa rikici bayan wasu mambobi sun zargi shugabanni da kokarin kakaba masu dan takarar ciyaman
- Masu zanga-zangar sun zargi kakakin majalisar Legas, Mudashiru Obasa, da kakaba wa karamar hukumar Ojokoro ɗan takara daga Agege
- Jagororin zanga-zangar sun bukaci a bai wa kowa dama tare da gargaɗin cewa damkawa baƙo tikiti zai haifar da matsala a jam’iyyar APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a karamar hukumar Ojokoro (LCDA) da ke jihar Legas ya rikide zuwa rikici a ranar Litinin.
An rahoto cewa rigima ta barke a ofishin jam'iyyar ne sakamakon zargin kakaba ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukuma da mutane ba sa so.

Asali: Twitter
Fusatattun 'ya jam'iyya sun hana taron APC
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa an fara taron jam'iyyar cikin lumana, da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai an ce 'yan mintuna da fara wannan taro, wasu fusatattun ƴan jam’iyyar suka mamaye dakin taron, tare da kaddamar da zanga-zangar adawa da manufar taron.
Masu zanga-zangar sun riƙa ihu da fadin kalmomi kalmomi kamar “’Barawo!”, “Ba za mu yarda ba!”, suna zargin kakakin majalisar Legas, Mudashiru Obasa, da kakaba wa Ojokoro ɗan takara daga yankin Agege.
Sauran kalmomin da suka dinga ambata sun haɗa da: “Wa ya san wani Sanusi?”, “Obasa ba zai mulke mu daga Agege ba”, da “Ba za mu yarda da baƙo ya jagorance mu ba”.
Abin da ya sa aka hargitsa taron APC
Daya daga cikin masu zanga-zangar, Mista Olusegun Akinoso-Olawaye, ya ce suna zargin jam'iyyar na kokarin kakaba masu ɗan takarar da ba shi da wata alaƙa da ƙaramar hukumar.
Ya jaddada cewa dole ne ɗan takarar shugabancin ƙaramar hukuma ya kasance mazaunin Ojokoro, ya zama dan cikin jam’iyyar kuma wanda ya san siyasar ƙaramar hukumar.
Mista Olusegun ya gargaɗi masu ruwa da tsaki na APC da cewa kakaba baƙo da ba shi da ilimi a harkar siyasar Ojokoro zai iya haifar da mummunar matsala.
“Mun zo nan ne domin mu nuna ƙin amincewarmu da nadin kama karya. Ya zama wajibi a kyale dukkanin 'yan takara su fafata da junansu bisa adalci,” inji Mista Olusegun.
Ya kara da cewa akwai akalla mutane 18 da ke neman kujerar shugaban karamar hukumar Ojokoro, kuma dukansu suna da magoya baya da suka halarci zanga-zangar.
Ana zargin jagororin APC da son kai
Hajiya Bola Ojetayo, wata daga cikin jagororin masu zanga-zangar, ta koka da cewa shugabannin jam’iyyar sun fi fifita muradunsu fiye da muradin jama’a.
Ta ce sun gudanar da zanga-zangar ne domin hana kakaba wani da mutanen Ojokoro ba su sani ba a matsayin shugaban ƙaramar hukumar na gaba.
“Ba za mu sayar da kujarmu ga baƙi ba. Baƙo ba zai zo ya jagorance mu a gidajenmu ba.
“Ba za mu yarda wasu su zauna a wani wuri su yanke hukunci a madadinmu ba. Mutumin da ke Agege ba zai zaɓa mana shugaba a Ojokoro ba."
- Inji Hajiya Ojetayo.
APC ta lallashi masu zanga-zanga a Legas

Asali: UGC
A martaninsa, Mista James Owolabi, tsohon ɗan majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar APC a Ojokoro, ya roƙi masu zanga-zangar da su guje wa tashin hankali.
Mista James, wanda ya wakilci mazabar Ifako-Ijaiye, ya amince da korafe-korafen jama’a, inda ya tabbatar da haƙƙinsu na bayyana ra’ayinsu a cikin jam’iyyar.
“Ku na da haƙƙi a cikin jam’iyyar APC. Ku na da 'yancin bayyana ra’ayinku cikin lumana ba tare da tashin hankali ba,” inji James.
Daga cikin sauran shugabannin APC da suka halarci taron har da Mista Jelili Oseni, shugaban ƙaramar hukumar da kuma tsohon ɗan majalisar jihar Legas, Ipoola Omisore.

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna
Shirin babban taron APC ya kankama
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan jam’iyyar APC sun yi tururuwa a sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja domin halartar babban taron da aka shirya.
An sanya tsauraran matakan tsaro a unguwannin kusa da Wuse 2 da kewaye, gabanin isowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zuwa wurin taron.
Daga cikin fitattun mutane da suka halarci harabar sakatariyar har da tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari da Honarabul Benjamin Kalu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng