Sharadin da Buhari Ya ba Atiku, El Rufa'i kafin Ganawa da Su a Kaduna

Sharadin da Buhari Ya ba Atiku, El Rufa'i kafin Ganawa da Su a Kaduna

  • Hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala ya bayyana yadda aka gudanar da taron tattauna wa tsakanin Muhammadu Buhari da su Atiku Abubakar
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ja tawaga, daga ciki har da Nasir El-Rufa'i domin kai ziyara ga tsohon shugaban Najeriya a gidansa da ke Kaduna
  • Daniel Bwala ya ce duk da Buhari ya amince da zaman, amma ya bayar da sharadin cewa sai an dauki hoto saboda kaucewa yada labaran karya
  • Hadimin Tinubu ya yi zargin cewa matakin da Buhari ya dauka ya dakile fitar da labarin cewa tsohon shugaban zai shiga SDP ko PDP bayan taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KadunaMai magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da sharadin tattaunawa da Atiku da tawagarsa.

Kara karanta wannan

'Hanya 1 ce': Atiku Ya Saɓa da Gwamnonin PDP kan Haɗaka da Tuge Tinubu a Mulki

Bwala ya bayyana cewa tsohon shugaban ya dage cewa sai an kawo kyamara domin daukar hoton ganawar da ya yi da wasu masu kawancen adawa da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Buhari
An fadi sharadin da Buhari ya bayar na gana wa da su Atiku Hoto: @atiku
Asali: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa Bwala ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a shafinsa na X bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, suka kai wa ziyara a gidansa da ke Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya sa sharadin ganawa da Atiku

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa Bwala ya bayyana cewa Buhari ya dage cewa sai an dauki hoton zaman, domin hana El-Rufai ya fito yana cewa wai Buhari ya amince da shiga jam’iyyar SDP.

Bwala ya ce tsohon shugaban kasar ya yi kokari sosai domin hana yaduwar wani labari daga bakin El-Rufai wanda zai iya bayar da wani labari da ba gaskiya ba game da ganawar.

Hadimin shugaban kasa ya bayyana cewa cewa:

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

“Sun tafi wajen Muhammadu Buhari kuma an ruwaito cewa ya dage sai an dauki hoton zaman a fili ko da kyamara, domin kada El Rufa'i ya fito ya ce Buhari na shirin shiga SDP ko PDP.

Sai dai babu wata hujja da Bwala ya kawo da ke tabbatar da wanan zance ko zargi da yake yi wa tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

Ana neman albarkar Buhari don tumbuke Tinubu

Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai dukkaninsu na cikin kawancen adawa da Tinubu, wanda ke shirin kifar da gwamnatin sa a zaben 2027.

Duk da cewa sun bayyana ziyarar da suka kai wa Buhari a matsayin gaisuwar Sallah, rahotanni na nuna cewa hakan ba zai rasa nasaba da burinsu na siyasa a shekarar 2027 ba.

Rahoton ya kara da cewa zaman ya kasance wani yunkuri na neman goyon bayan Buhari ko akalla hana shi bayyana goyon baya ga shugaban kasa mai ci a yanzu.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

An yi zargin Buhari yana kin Tinubu

A baya, kun samu labarin cewa sohon jigon jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa Bola Tinubu ya na sane da yadda Muhammadu Buhari ya yi masa bakin cikin zama shugaban Najeriya.

A cewar Galadima, Muhammadu Buhari bai yi murna ba da Tinubu ya samu takarar a APC, har ma ya samu nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a 2023 saboda ya bijire masa.

Ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan kiyayyar shi ne yadda Tinubu ya ki aiwatar da umarnin Buhari na tabbatar da cewa an kori Buba Galadima daga cikin kwamitin amintattun APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng