Sauya Sheka: Hadimin Buhari Ya ce za Su Yi Maraba da Kwankwaso a APC
- Magoya bayan jam’iyyu sun fara bayyana ra’ayoyinsu kan rade-radin da ke yawo cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai koma APC kafin zaɓen 2027
- Hadimin Muhammadu Buhari ya ce za su marabci Kwankwaso idan ya dawo APC, yayin da wasu suka ce hakan zai janyo ce-ce-ku-ce a siyasar Kano
- Tun a watan Janairu shugaban NNPP a Kano ya musanta zargin cewa Kwankwaso na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa APC mai mulki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Rahotanni na nuni da cewa tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a NNPP a 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, na shirin komawa APC.
Tun a farkon 2025 Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana cewa Rabiu Kwankwaso na neman hadin gwiwa da Shugaba Bola Tinubu domin karfafa gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Asali: Facebook
Hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa za su yi maraba da Rabiu Kwankwaso idan ya sauya sheka zuwa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai tun a watan Janairu, Daily Trust ta wallafa cewa jam’iyyar NNPP ta Kano ta musanta wadannan rade-radin.
'Za mu marabci Kwamkwaso a APC,' Bashir
Tsohon mai taimaka wa Shugaba Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa APC za ta yi maraba da Kwankwaso idan har ya dawo.
Bashir ya ce:
“Za mu yi maraba da Sanata Kwankwaso da mutanensa cikin jam’iyyarmu ta APC.”
Sai dai magoya bayan jam’iyyun sun bayyana ra’ayoyi mabambanta, Ibrahim Dauda Isa ya yi zargi da cewa:
"Dama Kwankwaso yana aiki da APC tun 2023."
Othman Ya’u ya yi gargadin cewa:
"Dawowarsa APC zai lalata masa siyasa."
Japhet Danbaba Laya ta yi tambaya da cewa:
"Ko wa zai kasance shugaban APC a Kano idan Kwankwaso ya dawo?"
Abu-Ammar Yareema ya yi hasashen cewa:
"Kwankwaso zai kwace jam’iyyar daga hannun Ganduje da magoya bayansa."

Asali: Facebook
Da gaske Kwankwaso zai koma APC?
Tun da aka fara rade radin a watan Janairu, shugaban NNPP na Kano, Hashim Dungurawa, ya bayyana cewa babu wani jigo da ke shirin komawa APC.
Ya ce:
“Gwamnanmu yana aiki, kuma shi ne gwamna mafi kwarewa a Najeriya yanzu. Me za mu ci idan mun bar NNPP muka koma APC?”
Dangane da kalaman Musa Iliyasu da ya ce Rabiu Kwankwaso zai koma APC, Dungurawa ya ce rade-radi ne kawai da ke neman tada zaune tsaye a siyasar jihar.
A yanzu haka dai ana sauraron ko NNPP za ta yi magana kan rade rade radin da ke yawo a kafafen sada zumunta game da sauya shekar Kwankwaso.
Shugabannin APC da NNPP sun koma SDP

Kara karanta wannan
Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin jam'iyyun NNPP da APC sun sauya sheka zuwa SDP a jihar Kaduna.
Legit ta rahoto cewa dukkan shugabannin jam'iyyun sun koma SDP ne a mazabar Kargi da ke karamar hukumar Kubau ta jihar.
SDP na kara karfi a jihar Kaduna da wasu yankunan Arewacin Najeriya tun bayan komawar Malam Nasir El-Rufa'i jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng