An Samu Ɓaraka a PDP, Ɗaruruwan Magoya bayan Babbar Jam'iyyar Adawa Sun Koma LP

An Samu Ɓaraka a PDP, Ɗaruruwan Magoya bayan Babbar Jam'iyyar Adawa Sun Koma LP

  • Jam’iyyar PDP ta gamu da babbar koma baya a jihar Abia, bayan daruruwan 'ya'yanta sun sauya sheka zuwa LP a yankin Ohafia
  • Hon. Sunday Anya Ojo, tsohon dan takarar majalisar jiha, ya jagoranci daruruwan magoya bayansa zuwa LP yana mai cewa 'PDP ta mutu'
  • Mataimakin gwamna Emetu ya karbi masu sauya shekar, yana cewa hakan ya kara karfin jam'iyyar LP gabanin zaben 2027 mai zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abia - Jam’iyyar PDP a jihar Abia ta fuskanci babbar koma baya yayin da daruruwan 'ya'yanta suka sauya sheka zuwa jam’iyyar LP.

Tsohon dan takarar kujerar majalisar dokoki kuma dan siyasa mai tasiri daga mazabar Isiama a Elu Ohafia, Hon. Sunday Anya Ojo, ne ya jagoranci sauya shekar.

Daruruwan magoya bayan PDP sun sauya sheka zuwa LP a jihar Abia
Dandazon magoya bayan PDP a wani babban taron jam'iyyar. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Daruruwan magoya bayan PDP sun koma LP

Kara karanta wannan

Tsufa ya zo da gardama: Dattijo ɗan shekara 50 ya ɗirka wa ƴarsa ciki a Bauchi

Hon. Ojo ya taba rike mukamin mai taimaka wa gwamna na musamman kan hada kan matasa har sau biyu a lokacin tsohuwar gwamnatin jihar, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da bikin sauya shekar ne a gidan mataimakin gwamnan jihar, Ikechukwu Emetu, da ke Amaekpu Ohafia a karamar hukumar Ohafia.

A lokacin da yake bayani kan dalilinsa na shigajam'iyyar LP a daidai wannan lokaci, Hon. Ojo ya ce PDP ta riga ta dusashe a siyasance a jihar Abia.

Dalilin 'yan PDP na komawa LP a Abia

Ya bayyana cewa ba zai iya ci gaba da zama a jam'iyyar da tauraruwarta ta dusashe a jihar ba, dole ne ya shiga jam'iyyar da ke ta karfi da tasiri.

Hon. Ojo ya kara da cewa yana da yakinin LP yanzu ta samu karbuwa sosai a jihar, tare da alwashin bada gudummawa wajen ganin jam’iyyar ta ci gaba.

Tsohon hadimin gwamnan ya ce:

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

“Na yanke shawarar barin PDP domin in shiga LP. Gaskiya PDP ta mutu a jihar Abia, jam'iyyar na cikin dakin ajiyar gawa yanzu."

Ya kara da cewa ya koma LP ne tare da dukkanin tubalin tafiyarsa ta siyasa domin hada karfi da karfe da sabuwar jam’iyyarsa.

Abia: LP ta yi maraba da tawagar PDP

Jam'iyyar LP ta yi maraba da daruruwan magoya bayan PDP suka sauya sheka a Abia
Hon. Ojo tare da tawagarsa a lokacin da suka sauya sheka daga PDP zuwa LP a Abia. Hoto: Alhaji K Mallam
Asali: Facebook

Mataimakin gwamnan jihar, Emetu, ya tarbi sababbin mambobin da hannu biyu, yana mai bayyana cewa hakan zai kara karfin LP a jihar.

Emetu ya yaba wa Hon. Ojo bisa jajircewarsa da karsashi wajen yanke irin wannan babban mataki na siyasa da kuma samun goyon bayan jama'arsa.

Wannan sauya sheka ya zama wani karin karfi ga LP a yankin Ohafia tare da nuna sauyin yanayin siyasar jihar gabanin zaben 2027.

Masu sharhi na ganin cewa sauya shekar Hon. Ojo da daruruwan mambobinsa na nuni da rugujewar tasirin PDP a jihar Abia.

Daruruwa sun watsar da PDP, sun shiga APC

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, daruruwan ƴaƴan jam’iyyar PDP a Nasarawa sun fice daga jam’iyyar, inda suka sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum 600 daga PDP da kuma jam’iyyar SDP ne suka rungumi APC a wani babban taron sauya sheka da aka shirya.

Kwamishinan muhalli da albarkatun kasa na jihar Nasarawa, Yakubu Kwanta, ne ya karɓi waɗanda suka sauya sheka a gundumar Ningo Bohar da ke Akwanga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng