El Rufa'i: Dukkan Shugabannin APC a Mazabar Kaduna Sun Koma SDP

El Rufa'i: Dukkan Shugabannin APC a Mazabar Kaduna Sun Koma SDP

  • Bayan sauya sheƙar El-Rufai daga APC zuwa SDP, jam’iyyar na ƙara samun karɓuwa a sassa daban-daban na jihar Kaduna
  • Dukkan shugabannin jam’iyyun APC da NNPP a gundumar Kargi ta ƙaramar hukumar Kubau sun fice zuwa jam'iyyar SDP
  • An kuma buɗe sabuwar sakatariyar SDP a Suleja, Jihar Neja, inda mutane da dama suka karɓi katin zama ‘yan jam’iyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Jam’iyyar SDP na ci gaba da samun karɓuwa a jihar Kaduna da ma wasu sassa na Arewacin Najeriya.

SDP na kara samun karbuwa a Najeriya ne bayan ficewar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyyar APC zuwa SDP.

SDP Kargi
Shugabannin APC da NNPP sun koma SDP a Kaduna. Hoto: SDP National Update
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda SDP ta kara karbar mutane a jihohi, musamman Kaduna ne a wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Abin ya fara damun Tinubu, an 'gano' shirinsa kan ƴan APC da ke son komawa SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin APC da NNPP sun koma SDP

A yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙaratowa, jam’iyyar SDP na kara shiga cikin harkokin siyasa da karfi a wasu ƙananan hukumomi da dama a jihar Kaduna.

Rahotanni daga gundumar Kargi a ƙaramar hukumar Kubau sun tabbatar da cewa gaba ɗaya shugabannin jam’iyyar APC da NNPP na yankin sun fice daga jam’iyyunsu zuwa SDP.

Kaduna: SDP ta kara samun karfi a Soba

A ƙaramar hukumar Soba, al’amura na kara canzawa. Jama’a da dama daga APC na ci gaba da komawa SDP.

Sanarwar da jagoran SDP ya fitar ta ce:

“Tun yanzu, ba na tunanin akwai wani lungu da jam’iyyar SDP ba ta shiga ba. Gashi kullum jama’a na rige-rigen ficewa daga APC suna shiga jam’iyyar SDP mai albarka.”

Haka zalika, a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, jam’iyyar SDP na ci gaba da samun karɓuwa daga masu ficewa daga jam’iyyu.

Kara karanta wannan

Duk da ikon da APC da shi a jihohi 21, Ganduje ya fadi shirin kwato ƙarin wasu

Jam'iyyar SDP ta bayyana cewa tana yawaita karɓar sababbin ‘yan jam’iyya a ko’ina cikin karamar hukumar.

SDP Kaduna
'Yan SDP yayin wani taro a Birnin Gwari. Hoto: SDP National Update
Asali: Facebook

An buɗe sabon ofishin SDP a jihar Neja

A daya bangaren kuma, jam’iyyar SDP ta buɗe sabon ofishi a ƙaramar hukumar Suleja ta jihar Neja.

A wajen buɗe ofishin, an samu gagarumar tarba daga jama’a, inda mutane da dama suka karɓi katin zama ‘yan jam’iyyar.

Tuni dai SDP ke bayyana shirinta na ceto al’umma daga halin da Najeriya ke ciki ta hanyar sauya tsarin shugabanci da dawo da amintaccen mulki.

Atiku da 'yan SDP sun ziyarci Buhari

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abuabakar tare da wasu jagororin SDP sun ziyarci Muhammadu Buhari a gidan da ya koma a Kaduna.

Cikin manyan jagororin SDP da suka taka wa Atiku baya sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i.

Yayin da yake hira da manena labarai bayan ziyarar, Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa akwai shirin hadakar 'yan adawa a Najeriya domin tunkarar Bola Tinubu a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng