2027: APC Ta Tabo Batun Ajiye Kashim Shettima, Ta ba Shugaba Tinubu Shawara

2027: APC Ta Tabo Batun Ajiye Kashim Shettima, Ta ba Shugaba Tinubu Shawara

  • Jam'iyyar APC reshen jihar Borno ta yi magana kan raɗe-raɗin da ke cewa Bola Tinubu zai sauya Kashim Shettima kafin zaɓen 2027
  • A cikin wata sanarwa da shugabannin jam'iyyar suka fitar, sun buƙaci Tinubu da ya ci gaba da tafiya da Shettima a matsayin mataimakinsa
  • Masu ruwa da tsakin na jam'iyyar APC mai mulki sun kuma nuna goyon bayansu ga manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Jam’iyyar APC reshen jihar Borno ta ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan Kashim Shettima.

Jam'iyyar APC ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya ci gaba da tafiya da mataimakin shugaban ƙasan a matsayin abokin takararsa a zaɓen shekarar 2027.

Tinubu da Kashim Shettima
APC ta bukaci Tinubu ya ci gaba da tafiya da Kashim Shettima Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

APC ta buƙaci Tinubu ka da ya ajiye Shettima

Jaridar The Cable ta rahoto cewa hakan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da shugaban APC, Bello Ayuba da sakataren jam'iyyar, Mustapha Loskuri suka fitar.

Kara karanta wannan

2027: Sabuwar tafiyar Atiku da El Rufa'i ta fara samun karbuwa a Neja Delta

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kiran na su dai ya zo ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin cewa shugaban ƙasa na iya sauya Kashim Shettima kafin zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta yi wannan kira ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Lahadi a gidan gwamnati da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

A cikin sanarwar, masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun yabawa sadaukarwar Shettima wajen goyon bayan manufofin Shugaba Tinubu.

Wane shawarwari jam'iyyar APC ta ba da?

“Wannan taro ya yi kira ga mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, da ya ci gaba da kasancewa mai biyayya ga shugaban ƙasa, da kuma ci gaba da hidima bisa gaskiya domin tallata manufofinsa.”
"Taron ya yi addu’ar cewa Allah Ya ba shugaban ƙasa ikon ci gaba da tafiya da Sanata Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a wa’adin mulki na biyu."
"Taron ya bayyana cikakken goyon baya da biyayya maras yankewa ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin mai girma shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu GCFR.”

Kara karanta wannan

Duk da ikon da APC da shi a jihohi 21, Ganduje ya fadi shirin kwato ƙarin wasu

“Taron ya kuma amince da shirin Renewed Hope na gwamnatin Tinubu. Ya yi fatan Allah Ya ɗora shugaban ƙasa da mataimakinsa a kan daidai, ya kare su, tare da basu nasara a wa’adin mulkinsu."

- Bello Ayuba

APC ta nuna goyon baya ga Zulum

Babagana Umara Zulum
APC a Borno ta nuna goyon baya ga Zulum Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, masu ruwa da tsakin jam’iyyar sun bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Babagana Umara Zulum na jihar Borno.

Sun kuma buƙaci ya ci gaba da jajircewa wajen ceto jihar daga hannun ƴan ta’adda, masu tayar da ƙayar baya da sauran miyagun laifuka.

Hadimin Tinubu ya ce Ndume zai bar APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun bakin shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ya yi wa Sanata Ali Ndume wankin babban bargo.

Daniel Bwala ya zargi Ndume da zama maci amana, inda ya ce yana yi wa ƴan adawa leƙen asiri a jam'iyyar APC.

Hadimin na Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa Ndume zai shiga cikin haɗakar ƴan adawa domin ruhinsa yana tare da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng