Rikicin PDP: An Gano Dalilin Adawar Atiku da Gwamnan Bauchi, Bala tun Zaben 2019

Rikicin PDP: An Gano Dalilin Adawar Atiku da Gwamnan Bauchi, Bala tun Zaben 2019

  • 'Dan gwamnan Bauchi, Shamsudeen Bala Mohammed ya fara nuna cewa mahaifinsa, ba zai mara wa Atiku Abubakar baya ba
  • Injiniya Shamsuddeen ya ce wannan ya biyo rawar da suke zargin Atiku ya taka wajen kokarin hana mahaifinsa samun nasara a zaben gwamnan Bauchi
  • Ya kara da cewa shekarar 2027, lokaci ne da zai ba Bala Mohammed damar yi wa Atiku sakayya da abin da aka yi masa a zaben 2023
  • 'Dan gwamnan, ya kawar da yiwuwar sulhu tsakanin mahaifinsa da Atiku Abubakar, saboda yana ganin ba a dauke su da muhimmanci ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi –Shamsudeen Bala, ya bayyana laifin da tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi wa mahaifinsa, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Ya ce zaɓen 2027 zai ba da dama ga mahaifinsa, Gwamna Bala Mohammed, ya biya Atiku Abubakar abin da ya yi masa a zaben 2023.

Atiku
Dan gwamnan Bauchi ya fadi kore hada kai da Atiku a zaben 2027 Hoto: @mahbeel_A
Asali: Twitter

Leadership News ta ruwaito cewa Injiniya Bala ya ce Atiku ya yi wa mahaifinsa zagon kasa bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa ya doke shi a zaben fitar da gwani na jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An zargi Atiku da watsi da gwamnan Bauchi

Daily Post ta ruwaito cewa ɗan gwamnan ya yi zargin cewa Atiku, duk da kasancewarsa a 'dan PDP, ya goyi bayan Sadique Abubakar, wanda shi ne dan takarar APC a zaben gwamnan Bauchi.

Ya ce:

“Atiku ya yi aiki tukuru don jawo wa mahaifina matsala wajen sake zabensa a matsayin gwamnan Bauchi a shekarar 2023. Ya tara manyan mutane da suka yi adawa da mu.”

Injiniya Bala ya ci gaba da cewa Atiku ba zai amince da sulhu tare da gwamnan Bauchi ba, saboda ba su da martaba a idon sa, kuma ba a dauke su a matsayin wadanda za su tabuka komai ba.

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

Makusantan Atiku sun samu matsala da gwamnan Bauchi

Rahoton ya ce a yayin yakin neman zabe na 2023 a jihar Bauchi, manyan ‘yan siyasa daga PDP sun mara wa 'yan adawa baya, a maimakon Bala Mohammed.

An yi hasashen daga cikin makusantan Atiku da suka yi adawa da takarar gwamnan Bauchi shi ne tsohon Wazirin Bauchi, Muhammadu Bello Kirfi.

Gwamna
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Hoto: Se. Bala AbdulKadir Muhammad
Asali: Facebook

Kuma tuni aka raba shi da matsayinsa na daya daga cikin masu nada sarakuna a masarautar Bauchi watanni kafin a gudanar da zaben.

Haka kuma ana zargin wani na hannun daman Atiku, Ahmed Mu’azu, da cewa shi ma ya taka rawa a kokarin hana Bala Mohammed samun nasara a zaben 2023.

Ana son gwamnan Bauchi ya tsaya takara

A baya, kun samu labarin cewa kungiyar gamayyar matasa da dattawan Kiristoci ‘yan siyasa ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan da yake yi.

Kungiyar ta kuma bayyana goyon bayanta dangane da shirinsa na tsayawa takara a babban zaben 2027, tare da shan alwashin mara masa baya idan ya nemi tsaya wa takara a zabe mai zuwa.

Shugabannin kungiyar, Joel Joshua da Ɗanladi Audu ne suka bayyana haka yayin wani taron a Bauchi, tare da tabbatar da cewa za su goyi bayan duk wanda za a tsayar takara a Bauchi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel