2027: Sabuwar Tafiyar Atiku da El Rufa'i Ta Fara Samun Karbuwa a Neja Delta
- Hadin kan siyasa da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai ke jagoranta ya fara jan hankalin shugabannin yankin Niger Delta domin ƙirƙirar sabuwar tafiya a 2027
- An ce sun tuntuɓi tsofaffin shugabannin yankin da wasu fitattun masu ta da kayar baya da suka ajiye makamansu tun 2009 domin neman goyon bayansu
- Fadar shugaban ƙasa ta magantu kan yunkurin da suka fara, tana mai cewa Bola Tinubu d aKashim Shettima sun fi maida hankali kan kawo cigaba a yanzu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, sabuwar tafiyar da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da Aminu Waziri Tambuwal ke jagoranta ta fara shiga yankin Niger Delta.
A yayin da Atiku Abubakar ya ziyarci Muhammadu Buhari a Kaduna a makon da ya wuce, ya bayyana cewa akwai shirin sabuwar tafiya a siyasar 2027.

Asali: Facebook
A cewar rahoton Leadership, a shirin 'yan siyasar na fuskantar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027, sun fara tuntuɓar manyan mutane daga yankin Neja Delta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa Atiku ya samu haɗin kan wasu tsofaffin shugabannin Neja Delta, wadanda ke jagorantar shirin yaɗa manufa da tuntuɓar shugabanni a yankin.
Ƙoƙarin shawo kan masu zabe a Neja Delta
Rahoton ya nuna cewa tafiyar ta fara samun karɓuwa daga manyan shugabannin yankin, musamman bayan ayyana dokar ta-baci a Rivers wacce ta kai ga dakatar da Gwamna Fubara
An ruwaito cewa lamarin ya fusata al’ummar Ijaw, wanda hakan ya bai wa 'yan siyasar damar tunkarar su da tayin haɗin gwiwa.
Wasu tsofaffin shugabannin kungiyoyin masu tayar da kayar baya ma sun fara tallata manufar tafiyar a jihohin Bayelsa, Rivers, Edo da Ondo.

Asali: Twitter
Fadar shugaban kasa ta mayar da martani
Da yake martani kan lamarin, mai magana da yawun ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, ya cewa a yanzu Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima ba sa damuwa da batun 2027.
Ya ce:
“A halin yanzu, abin da ya fi damun shugaban ƙasa shi ne farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da ci gaba ga 'yan Najeriya, ba maganar neman tazarce ba.”
Wani hadimi ga Atiku a Bayelsa, Timi Frank ya tabbatar da cewa tafiyar na samun gagarumin goyon baya daga yankin Kudu maso Kudu da Kudu.
A cewarsa:
“Wannan tafiya mai ƙarfi ce. Mutane da dama sun gaji da halin da ake ciki, kuma wannan tafiya za ta ba da mamaki a Najeriya nan da 2027.”
Ganduje ya ziyarci Buhari a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna.
Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa APC ba za ta ji tsoron shirin hadakar da 'yan adawa ke yi a Najeriya ba.
Jiga jigan APC sun ziyarci Muhammadu Buhari ne jim kadan bayan wasu 'yan adawa da suka hada da Atiku Abubakar sun ziyarce shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng