Duk da Ikon da APC da Shi a Jihohi 21, Ganduje Ya Fadi Shirin Kwato Ƙarin Wasu

Duk da Ikon da APC da Shi a Jihohi 21, Ganduje Ya Fadi Shirin Kwato Ƙarin Wasu

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar na ƙoƙarin samun ƙarin jihohi fiye da guda 21
  • Ganduje ya bayyana cewa APC za ta iya cimma hakan ta hanyar haɗin gwiwar siyasa ko kuma ta hanyar nasarar zaɓe a sauran jihohi 3
  • Ya ce ko da suna da iko kan jihohi 21, amma suna hangen wasu jihohi su shigo musu ta hanyoyi daban-daban
  • Wannan bayani ya fito ne yayin da ‘yan adawa ke ƙoƙarin haɗewa domin ƙwace mulki daga APC kafin zaɓen 2027 mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje, ya bugi kirji kan kokarin kwato wasu jihohi a Najeriya.

Ganduje ya ce suna shirin faɗaɗa mulkinsu fiye da jihohin 21 da suke rike da su yanzu.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan APC ya fadi matsayar jam'iyyar kan hadakar 'yan adawa

Ganduje ya fadi shirin APC kan karɓe wasu jihohi
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce APC za ta karbe wasu jihohi a Najeriya. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Facebook

Ganduje ya fadi haka ne da yake magana da manema labarai kan siyasa, kasar yadda rahoton Tribune ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan adawa sun ziyarci Buhari a Kaduna

Shugaban APC ya fadi haka ne yayin da jam’iyyun adawa ke shirin haɗuwa kafin zaɓen 2027 domin su ƙwace mulki daga hannun APC.

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kadun.

Atiku ya jagoranci ƴan siyasa da suka hada da sohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal zuwa gidan Buhari.

Sheikh Isa Ali Pantami da Abubakar Malami su ma sun kai ziyarar Sallah ga tsohon shugaban, suna addu’ar Allah ya karbi ibadar da aka yi a Ramadan.

Ganduje ya ziyarci Buhari a Kaduna
Abdullahi Ganduje ya soki shirin haɗaka inda ya babu abin da za su yiwa APC. Hoto: @OfficialAPCNg.
Asali: Twitter

Ziyarar Ganduje zuwa ga Buhari a Kaduna

Daga bisani, shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar jiga-jigan jam’iyyar zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Babban kusa a APC ya ba 'yan adawa sirrin kayar da Tinubu a 2027

Ziyarar ta biyo bayan zuwan shugabannin jam’iyyun adawa PDP da SDP da suka hada da Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i.

Yayin taron, Ganduje ya tabbatar da cewa babu abin da jam'iyyun adawa za su iya yi wa APC mai mulkin Najeriya kawai bata lokacinsu suke yi.

Ganduje ya bugi kirji kan shirin APC

Tsohon gwamnan Kano ya bayyana cewa jam’iyyar na da ƙarfi kuma tana fatan ƙara samun rinjaye a faɗin ƙasar nan.

Ya ce:

“Ko da muna magana da jihohi 21, amma muna hangen wasu jihohi su shigo mana, ko gwamnoninsu su dawo, ko kuma mu kayar da su.”

Wani ɗan PDP a Gombe ya fadawa Legit Hausa yadda APC take a yanzu.

Aliyu Muhammad ya ce duba da yadda jam'iyyar ke tafiya a yanzu komai na iya faruwa kan jihohin da take gadara da su.

Ya ce:

"Jihohi 21 da take tutiya da su din ma tana iya rasa wasu daga ciki saboda salon shugabancinta."

Kara karanta wannan

Abin ɓoye ya fito fili: Jerin sunayen Yarbawa 140 da Tinubu ya ba manyan muƙamai

Aliyu ya shawarci PDP da ta yi amfani da matsalar APC domin gyara barakar da ke cikinta da kwace mulki.

Tsohon bidiyon Ganduje na sukar Buhari ya bayyana

A baya, kun ji cewa an sake dawo da tsohon bidiyon shugaban APC a yanzu, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana caccakar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kan sauya kudi kafin zaben 2023.

A cikin bidiyon, Ganduje na cewa Buhari yana son hana zabe ne, inda ya zarge shi da lalata jam’iyyar da ta tallafa masa wajen hawa mulki bayan shan kaye a lokuta da dama a baya.

Ganduje ya ce babu amfani a sauya takardun kudi a wancan lokaci inda ya ce shirin na Buhari tamkar kokari ne na hana yin sahihin zabe bayan shi kuma ya kammala wa'adinsa biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel