Wata Sabuwa: PDP Ta Ki Amincewa da Murabus din Kakakinta, Ta Fadi Dalili

Wata Sabuwa: PDP Ta Ki Amincewa da Murabus din Kakakinta, Ta Fadi Dalili

  • Jam'iyyar adawa PDP a jihar Ondo ta ƙi amincewa da murabus ɗin sakataren yaɗa labaranta, Kennedy Peretei
  • Shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na PDP a Ondo, Bakitta Bello, ya jagoranci wata tawaga zuwa gidan Peretei domin ba shi baki
  • Bakitta Bello ya buƙaci sakataren yaɗa labaranta ɗa ya janye buƙatarsa ta yin murabus domin ba za su yarda da ita ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Jami’iyyar PDP reshen jihar Ondo ta bayyana matsayarta kan murabus ɗin da mai magana da yawun bakinta, Kennedy Peretei ya yi.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa ba ta amince da murabus ɗin da Kennedy Peretei ya yi ba daga matsayin mai magana da yawun bakin jam’iyyar.

Kennedy Peretei ya yi murabus daga PDP
PDP ta yi watsi daurabus din sakatarenta a Ondo Hoto: Kennedy Peretei
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta rahoto shugaban kwamitin riƙon ƙwarya na PDP a jihar Ondo, Bakitta Bello, ya bayyana hakan a ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

"Akwai talauci a Najeriya": Peter Obi ya fadi yadda rayuwa ta sauya masa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa sakataren PDP ya yi murabus?

A rarar Laraba, Kennedy Peretei ya miƙa takardar murabus dinsa ga jam’iyyar PDP a mazaɓar Arogbo ta 1, cikin ƙaramar hukumar Ese Odo.

A cikin takardar murabus ɗin, ya bayyana cewa dalilinsa na barin muƙaminsa ya ta’allaka ne da abin da ya kira rashin adalci da son kai a shugabanci da ake nunawa.

Ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar na jihar ba su da niyyar lashe zaɓe, inda ya kwatanta halin da jam’iyyar ke ciki da cewa PDP ta kama hanyar zama gawa.

PDP ta ƙi amincewa da batun murabus

Sai dai a ranar Juma’a, shugaban kwamitin riƙon kwarya na PDP a jihar, Bakitta Bello, ya jagoranci wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa gidan Kennedy Peretei da ke Akure, domin ƙoƙarin shawo kansa ya janye murabus ɗin.

Bakitta Bello ya bayyana cewa shugabancin jam’iyyar PDP bai gamsu da hujjojin da Kennedy Peretei ya bayar ba dangane da dalilinnsa na barin muƙamin.

Kara karanta wannan

Mai magana da yawun PDP ya yi murabus daga muƙaminsa, ya tona asirin wasu shugabanni

Ya ce babu wani yanayi a halin yanzu da zai sa a ɗauki matakin da ya ɗauka, musamman duba da irin gudunmawar da ya bayar ga jam’iyyar tun daga farko.

"Haƙiƙa ka na da ƴancin jin haushi idan kana buƙatar hakan, amma dole ne ka fahimci cewa, a siyasa, abubuwa da dama na faruwa kafin a yanke hukunci."
"Kai ɗan jam’iyya ne na gaskiya, kuma hakan ne dalilin da ya sa muka zo gare ka domin ka sauya ra’ayinka.
"Muna buƙatar ka janye wannan murabus ɗin domin ba za mu karbi takardar murabus ɗinka ba."

- Bakitta Bello

Umar Iliya Damagum
PDP ta ki amincewa da murabus din sakatarenta a Ondo Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Facebook

A ƙarshe, Bakitta Bello ya buƙaci Peretei da ya ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar domin ci gaba da aikin gina jam’iyyar tare da tabbatar da nasararta a zaɓe na gaba.

Wannan yunƙuri na jam’iyyar ya nuna irin muhimmancin da suke bai wa Kennedy Peretei a matsayin babban jigo mai muhimmanci.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna ya yi gaban kansa, ya kaddamar da yakin neman sake zaben Tinubu

Ɗan majalisa ya sauya sheƙa zuwa PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta samu ƙaruwa bayan ɗan majalisar dokokin jihar Enugu ya sauya sheƙa zuwa cikinta.

Eze Gabriel na jam'iyyar LP wanda ke wakiltar mazaɓar Isi-Uzo ya tattara ƴan komatsan zuwa jam'iyyar PDP mulki a jihar.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ba a son ransa ya bar jam'iyyar LP ba, sai dai don wasu abubuwa da suka fi ƙarfinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng