Ganduje Ya Yi wa Atiku da El Rufa'i Raddi Mai Zafi a Gidan Buhari kan Zaben 2027
- Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce yunƙurin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun adawa ba zai kai ko ina ba
- Dr. Ganduje ya bayyana haka ne bayan ziyarar Sallah da shugabannin APC suka kai wa Buhari a gidansa da ke Kaduna
- Ganduje ya jaddada cewa APC tana da karfi kasancewar tana da gwamnoni 21 kuma za ta ci gaba da faɗaɗa tasirinta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Shugaban APC, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya yi watsi da yunƙurin haɗin gwiwa tsakanin 'yan adawa kafin zaɓen 2027, yana mai cewa lamarin ba zai kai ga nasara ba.
Ganduje ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, lokacin da mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa na APC (NWC) suka kai wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ziyarar Sallah.

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Asali: Twitter
Da yake magana da tashar Arise TV, Ganduje ya ce APC ba ta damu da yunƙurin haɗin kai ba, yana mai cewa irin wannan abu ya taɓa faruwa a baya amma bai yi nasara ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Ba mu damu da hadin gwiwarsu ba,' Ganduje
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya ce 'yan adawa na kulla wani shirin da ba zai kai ga nasara ba a 2027.
Ganduje ya ce:
“Tarihi ne ke neman maimaita kansa. Suna son shiga wani tsarin da ba zai yi aiki ba.
'Domin bisa abubuwan da muke gani, akwai sabani a tsakaninsu kuma ba za su iya zama tsintsiya madaurinki ɗaya ba.”
Ya ƙara da cewa:
“Mun fahimci siyasa sosai, kuma ba za mu bayyana dabarunmu ba, amma za mu nuna cewa mun shirya.”
Shugaban APC ya ce jam’iyyarsu na da gwamnoni 21 a yanzu kuma har yanzu ita ce mafi ƙarfi a yammacin Afirka.

Kara karanta wannan
"Akwai damuwa," Sanata Ndume ya yi magana kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027
Abdullahi Ganduje ya kara da cewa suna da burin faɗaɗa ikon jam’iyyar APC a wasu jihohi kafin 2027.
Shugaban APC ya yi martanin ne bayan Atiku Abubakar ya tabbatar da cewa akwai shirin hadaka a tsakanin 'yan adawa.

Asali: Twitter
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne yayin da ya kai wa Buhari ziyara tare da wasu manyan ‘yan siyasa, ciki har da tsofaffin gwamnoni Nasir El-Rufai, Aminu Tambuwal, Gabriel Suswam.
Tsohon gwamnan Adamawa, Jibrilla Bindow da tsohon gwamnan Imo Achike Udenwa na cikin wadanda suka taka wa Atiku baya.
Maganar wariya a mulkin Tinubu
Abdullahi Ganduje ya ce babu wariya ko fifita wani yanki a kan yadda Bola Tinubu ke nada mukamai.
Ya bayyana cewa a nan gaba kadan za su bayyana wa duniya yadda Bola Tinubu ya raba mukamai a Najeriya.
2027: An gargadi masu neman sauya Shettima
A wani rahoton, kun ji cewa wani jigo a APC, Farfesa Haruna Yerima ya gargadi masu kira da a sauya Kashim Shettima kafin 2027.

Kara karanta wannan
"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari
Farfesa Yerima ya ce hakan ya saba tsarin siyasa da aka gina a Najeriya tun dawowar dimokuradiyya a 1999.
Ya kara da cewa kasancewar Janar Yakubu Gowon da Janar Ibrahim Badamasi Babangida sun fito daga Arewa ta Tsakiya za a fahimci ba a ware yankin ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng