"Akwai Damuwa," Sanata Ndume Ya Yi Magana kan Haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027
- Sanata Ali Ndume ya ce bai kamata shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi sakaci da shirin ƴan adawa na haɗewa wuri ɗaya gabanin 2027 ba
- Ali Ndume ya bayyana cewa yunkurun haɗakar ƴan adawa babbar barazana ce ga tazarcen Bola Tinubu kuma ya kamata a ɗauki lamarin da gaske
- Sanatan ya ce akwai abubuwan da ya kamata Shugaba Tinubu ya damu da su musamman duba da halin matsin da tattalin arzikin da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ali Ndume ya bayyana cewa ya kamata shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan yunkurin ƴan adawa na haɗewa domin yaƙarsa a 2027.
Sanata Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu ya ce haɗakar ƴan adawa ba ƙaramar barazana ba ce ga burin Shugaba Tinubu na neman tazarce a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

Asali: Facebook
Sanatan ya yi wannan furuci ne a cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin na Channels tv ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2027: Yadda ƴan adawa ke shirin haɗaka
Idan ba ku manta ba jagororin jam'iyyun adawa a Najeriya sun tabbatar da shirinsu na haɗewa wuri guda domin kalubalantar Bola Tinubu da APC a 2027.
Ana ganin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, tsohon ɗan takarar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na cikin wannan haɗaka da ake shirin yi.
A hirar da aka yi da shi, Sanata Ndume ya ce ya kamata Tinubu ya damu idan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ya tare da shi a zabe mai zuwa.
Daily Trust ta ruwaito Ndume na cewa:
“Ko da yake Buhari kuri’a ɗaya gare shi, amma har yanzu yana da matukar tasiri a Arewacin Najeriya. Kuma idan bai kasance tare da Tinubu ba a 2027, hakan na da illa.”
Wace damuwa Tinubu zai iya fuskanta?
Ya kuma kara da cewa akwai dalilai da dama da za su sa Tinubu ya damu, inda ya ci gaba da cewa:
“Akwai dalilai na zahiri da na yanayi da ke nuna akwai damuwa, alal misali yanayin matsin tattalin arziki, hauhawar farashi da karyewar darajar Naira.
"Haka nan kuma idan ka duba, fadar shugaban kasa ta gaza hada kan jama’a, musamman ‘yan siyasa, yadda ya kamata, wannan ba ƙaramin abin damuwa ba ne.”

Asali: Facebook
"Ba na tsoron faɗar gaskiya" - Ndume
Sanatan ya bayyana cewa yana sane da cewa kalamansa za su janyo ce-ce-ku-ce, amma bai damu ba.
“Na fada hakan tun da farko a wani shiri na Arise TV, kuma ba na jin tsoron fadin gaskiya.”
Tuni dai wasu na kallon wadannan kalamai na Ndume a matsayin gargadi ga shugaba Tinubu da jam’iyyarsa ta APC, yayin da siyasar 2027 ke kara daukar zafi tun yanzu.

Kara karanta wannan
"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari
Ndume: Abin da ya sa ake ziyartar Buhari
A wani labarin, kun ji cewa Ali Ndume ya ce ziyarar da manyan ƴan siyasa ke kai wa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba abin mamaki ko sabon abu ba ne.
Sanata Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a inuwar APC, ya ce a zahirin gaskiya shi kansa zai ziyarci Muhammadu Buhari nan ba da jimawa.
Ya ce ƴan Najeriya na kai wa tsofaffin shugaban ƙasa ziyara a kai a kai, ba a kan Buhari aka fara ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng