Bayan Atiku Ya Gana da Buhari, an Karfafawa Uba Sani, Tinubu Guiwa a 2027
- Jiga-jigan APC a Kaduna sun bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu da Gwamna Uba Sani a zaben shekarar 2027
- Taron jiga-jigan APC ya mayar da hankali kan tsaro da ci gaba a yankin karamar hukumar Kachia da ke jihar
- Shugaban Karamar Hukumar ya bayyana cewa SDP ba za ta iya kawo cikas ba ga APC mai mulkin jihar da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Jiga-jigan jam’iyyar APC a jihar Kaduna sun nuna goyon baya ga Bola Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.
Masu ruwa da tsakin a karamar hukumar Kachia sun bayyana cikakken goyon bayansu ga shugaban da Gwamna Uba Sani, suka ce suna goyon bayan ci gaban mulkinsu bayan 2027.

Asali: Twitter
APC ta nunawa Tinubu da Uba Sani gata
Wannan matsaya ta fito ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a harabar ofishin hukumar karamar hukumar Kachia, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun ce an shirya taron ne domin karɓar bayanai dangane da harkokin tsaro da ci gaba a yankin.
Bayan kammala taron, Shugaban karamar hukumar kuma shugaban kungiyar jiga-jigan APC, Dr. Manzo Maigari, ya ce wannan dandalin yana ba da dama wajen sadarwa da juna tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya ce:
Mun yi wa jiga-jigan bayani game da ci gaban tsaro, sabuwar Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da kuma wasu nasarorin ci gaba.
“Bayan nazari kan yanayin siyasa a Kachia, jiga-jigan sun amince da cewa Shugaba Tinubu da Gwamna Uba sun cancanci ci gaba bayan 2027."

Asali: Twitter
APC ta caccaki SDP da jigonta, El-Rufai
Maigari ya kuma bayyana cewa jam’iyyar SDP da tsohon Gwamna Nasir El-Rufai ke mara wa baya ba za ta dawwama ba a siyasa, Vanguard ta ruwaito.
Ya bayyana jam’iyyar PDP a matsayin babbar jam’iyyar hamayya, amma ya nuna kwarin gwiwa da ikon APC a yankin da Kudancin Kaduna.
Ya kara cewa:
“Zan iya tabbatar muku cewa yankin Zone 3 da abokan huldar mu za su dawo da Shugaban kasa da Gwamna a 2027.
“Idan aka dubi nasarorin da muka samu a yankin, da wuya wani ya iya shawo kan mutanen Kudancin Kaduna su canza hanya.
“Cikin watanni 24 da jami’ar ta fara aiki, ana sa ran mutane 30,000 za su shiga Kachia, a cikin shekaru 3 zuwa 4, adadin na iya haura 100,000.”
Maigari ya yabawa rundunar soji bisa inganta tsaro, inda ya ce an rage matsalar rashin tsaro da kashi 80 bisa dari a Kudancin Kaduna.
Atiku, El-Rufai sun gana da Buhari
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya kai ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Kaduna.
Atiku ya jagoranci manyan mutane ciki har da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal.
Har ila yau, Sheikh Isa Ali Pantami da Abubakar Malami suma sun kai ziyarar Sallah ga tsohon shugaban kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng