'Renewed Hope': Daniel Bwala Ya Fadi Jihar da Ke Goyon bayan Tinubu 100 bisa 100
- Daniel Bwala ya bayyana cewa mutanen Kudancin Borno suna goyon bayan manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta Renewed Hope
- An karrama Bwala saboda gudummawarsa wajen samar da hadin kai da ci gaban Kudancin Borno, abin da Tinubu ya kira da 'ci gaban jihar'
- Bwala ya ce karramawar da aka yi masa ta nuna cewa al’ummarsa na tare da Tinubu kuma suna maraba da sauye-sauyen da yake kawowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Daniel Bwala, ya ce al'ummar shiyyar Kudancin Borno suna goyon bayan manufofin Shugaba Bola Tinubu na Renewed Hope Agenda 100 bisa 100.
Bwala, shi ne mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yada labarai da tsare-tsare, kuma dan asalin yankin Kudancin Borno ne.

Asali: Twitter
An karrama Bwala a Kudu maso Gabashin Borno

Kara karanta wannan
Abin da aka fadi ga Tinubu, Matawalle bayan aika riƙakken ɗan ta'adda lahira a Zamfara
Wannan na zuwa ne yayin da masu ruwa da tsaki na Kudancin Borno suka karrama Bwala da lambar girmamawa, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce an karrama mai ba shugaban kasar shawara saboda “gagarumar gudummawarsa wajen hadin kai, ci gaba, da bunkasar yankin da jihar Borno gaba daya.”
Bwala, yana daga cikin jiga-jigan mutane 16 na yankin Kudancin Borno da aka karrama don yabawa kyakkyawan aikinsu a hidimtawa al’umma.
Sauran manyan da aka karrama sun hada da tsohon hafsan rundunar sojin kasan Najeriya, Janar Tukur Buratai (mai ritaya).
Tinubu ya jinjinawa Bwala da aka karrama shi
Da yake jawabi a lokacin bikin karramar, Shugaba Tinubu, wanda ya samu wakilcin ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ya ce:
“Na yi farin ciki da Daniel Hasan Bwala ya kasance daya daga cikin wadanda aka karrama a wannan dakin a yau. Shi kamar ɗa ne a waje na."
Shugaba Tinubu ya ce wannan babbar karramawa da aka yi wa Bwala da sauran masu karbar kyautar alama ce ta ci gaban Kudancin Borno, jihar, da Najeriya baki daya.
“Sadaukarwarku, jajircewa, da kwarewa sun taimaka muka kai wannan matsayin. Abin farin ciki ne yadda aka karrama ku saboda ci gaban da kuka kawo wa wannan shiyya.
“Karramar da aka yi maku a yau, alama ce ta aikin da kuke yi tukuru, da jajircewa wajen ganin wadanda suka shirya wannan taro da ma al'ummar shiyyar sun samu rayuwa mai kyau."
- Shugaba Tinubu.
"Mutanenmu na tare da Tinubu 100 bisa 100' - Bwala

Asali: Twitter
Da yake magana da manema labarai bayan bikin, Bwala, wanda aka karrama, ya ce ya yi farin ciki da samun wannan lambar yabo daga masu ruwa da tsaki na shiyyarsa.
A cewar mai ba shugaban kasar shawara, karrama shi da aka yi alama ce ta mutanen Borno sun amince da gwamnatin Tinubu da sadaukarwar ta na gyara Najeriya.
“Na yi imanin cewa mutanen Kudu Maso Gabashin Borno suna tare da Shugaba Bola Tinubu 100 bisa dari, kuma suna goyon bayan manufarsa ta Renewed Hope."

Kara karanta wannan
Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027
Kudancin Borno na kunshe da kananan hukumomi tara, wato: Askira/Uba, Bayo, Biu, Chibok, Damboa, Gwoza, Hawul, Kwaya Kusar da Shani.
Tinubu ya saka wa Bwala da babban mukami
A wani labarin, mun ruwaito cewa, bayan dogon jira, an nada Daniel Bwala a matsayin hadimin Shugaba Bola Tinubu a ranar Alhamis, 14 ga Nuwamba, 2024.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Bwala a matsayin hadimi na musamman kan harkokin sadarwa tsare-tsare.
Nadin ya zo ne bayan watanni da Bwala ke yabawa manufofin gwamnatin Tinubu, tun bayan da ya bar tsohon ubangidansa, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng