PDP Ta Fasa Zaben Shugabanni a Shiyyoyi 3, Ta Aika Sako ga INEC da Ƴan Jam'iyyar

PDP Ta Fasa Zaben Shugabanni a Shiyyoyi 3, Ta Aika Sako ga INEC da Ƴan Jam'iyyar

  • Jam’iyyar PDP ta dage zabukan Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma saboda kisan da aka yi a jihar Filato kwanan nan
  • Hon. Debo Ologunagba ya ce dagewar za ta ba da dama ga gwamnonin yankuna su halarci taron PDP a Ibadan daga 13 zuwa 14 ga Afrilu, 2025
  • PDP ta ce sabuwar ranar zabenta na Kudu maso Yamma ita ce Laraba, 16 ga Afrilu, amma za a a sanar da lokacin zaben sauran yankuna nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar PDP ta sanar da dage zabukan da ta shirya yi a Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma har zuwa wani lokaci.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Hon. Debo Ologunagba ya fitar ranar Alhamis, 10 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

Turji ya sauya salo, an gano ƴan ta'adda na shiga Sokoto daga dazukan Zamfara

Jam'iyyar PDP ta bayyana dalili da ta dage zabukan shugabanninta a shiyyoyi 3
Jam'iyyar PDP ta dage taro a shiyyoyin Kudu da Arewa kan kisan mutane a Filato. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

PDP ta dage zabuka a Arewa da Kudu

Jam'iyyar ta wallafa wannan sanarwa a shafinsa na X, mai dauke da taken: 'PDP ta dage zabukan yankin Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu da Kudu maso Yamma.'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Hon. Debo Ologunagba ya ce tun tuni PDP ta shirya gudanar da zabukan ne a ranar Asabar, 12 ga Afrilu, 2025, amma yanzu an dage zabukan.

Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa kisan bayin Allah da aka yi kwanan nan a jihar Filato ne ya janyo daukar wannan mataki na dakatar da zabukan.

Hon. Ologunagba ya ce:

“An dakatar da zabukan ne domin nuna alhini tare da jajanta wa mutanen jihar Filato kan wannan kisan gillar da ya faru.”

Gwamnonin PDP za su yi taro a Ibadan

Hakanan, jam’iyyar ta ce dage zabukan zai ba gwamnonin yankunan damar halartar taron kungiyar gwamnonin PDP ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zariya da wani magidanci ya kashe ɗan uwansa da duka

Sanarwar Hon. Ologunagba ta ce an shirya gudanar da taron gwamnonin ne a Ibadan, jihar Oyo, daga Lahadi, 13 zuwa Litinin, 14 ga Afrilu, 2025.

Saboda haka, jam’iyyar ta sake sanya ranar Laraba, 16 ga Afrilu, a matsayin sabuwar rana don gudanar da zabe a Kudu maso Yamma.

Amma kuma, PDP ta ce za ta sanar da sababbin ranakun zabukan shugabanninta a Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu nan gaba kadan.

PDP ta aika sako ga INEC da 'yan jam'iyyar

Sakataren watsa labaran PDP ya magantu kan dage zabukan shugabannin PDP a shiyyoyi 3
PDP ta aika sako ga INEC da 'yan jam'iyyar bayan dage zaben shugabanni a shiyyoyi 3. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Jam’iyyar ta bayyana cewa kwamitin riko na Kudu maso Kudu karkashin jagorancin Chief Emmanuel Ogidi zai ci gaba da aiki.

"Kwamitin zai ci gaba da gudanar da harkokin yankin bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa kwaskwarima a shekarar 2017."

- Hon. Ologunagba.

PDP ta bukaci shugabanni, mambobi da duk masu ruwa da tsaki da su kula da wannan canji da aka samu, su kuma bi tsarin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027

Sanarwar ta ce:

“Ina sanar da hukumar INEC, ‘yan jarida, jami’an tsaro da daukacin al’umma da su dauki wannan sanarwa da muhimmanci."

Karanta sanarwar a nan kasa:

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.