CPC: Ana Hasashen Ficewar Mutanen Tsohon Shugaban Kasa Buhari daga APC

CPC: Ana Hasashen Ficewar Mutanen Tsohon Shugaban Kasa Buhari daga APC

  • Ziyarar da wasu daga cikin gwamnonin APC suka kai wa Muhammadu Buhari ta bar baya da tambayoyi game da ainihin dalilin ganawa da shugaban
  • APC na fuskantar kalubale, yayin da wasu daga cikin manyan 'yan jam'iyyar ke shirin bin sawun tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai zuwa SDP
  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin Ministocin Buhari na kokarin tattara kayansu domin ficewa daga cikin APC nan gaba kadan
  • A ziyarar da gwamnonin suka kai masa, sun roki tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sa baki wajen dakile shirin sauyin shekar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – An fara fargaba kan yiyuwar ficewar bangaren CPC daga jam’iyya mai mulki ta APC domin nema wa kansu mafita.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An gano asalin abin da ya kai gwamnonin APC wurin Buhari a Kaduna

Lamarin ya kara kamari musamman bayan wata ganawa da ta gudana a ranar Litinin a Kaduna tsakanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni na APC.

Buhari
An gano dalilin gwamnonin APC na ziyartar Buhari Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a da, an dauki ziyarar a matsayin ta girmamawa ga tsohon shugaban, amma kalaman gwamnonin ya sa an fara hasashen akwai babban al'amari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano cewa gwamnoni sun roki Buhari da ya shiga tsakani domin dakile ficewar jiga-jigai daga jam’iyyar, musamman daga bangaren CPC.

An roki Buhari kan ficewar ‘yan CPC a APC

Jaridar Vanguard ta bayyana cewa rokon da gwamnoni suka yi ya samo asali ne daga karuwar damuwa game da yiwuwar ficewar wasu 'yan jam'iyya kafin babban zaben shekarar 2027.

Tsohuwar CPC, wacce ta hade da wasu domin kafa APC, na daga cikin ginshikan jam’iyyar mai mulki, kuma ana kallon Buhari a matsayin jagora mafi tasiri a cikinta.

Buhari
Wasu gwamnoni sun ziyarci Buhari Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Akwai fargaba kan cewa ficewar wannan bangare na iya janyo gagarumar koma baya ga jam’iyyar a matakin kasa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari kan daliban jami'a a Kebbi cikin dare

Ganawar da aka yi a ranar Litinin ta zo ne a daidai lokacin da abokan siyasar Buhari ke ta sauya sheka daga APC zuwa SDP.

Ana hasashen ficewar masoya Buhari daga APC

Rahotanni sun ce wasu daga cikin tsofaffin ministocin Buhari suma suna shirin komawa SDP, kuma tuni aka samu wadanda suka bar APC a jihar Katsina, inda Buhari ya fito.

CPC jam’iyya ce da aka kafa a shekarar 2009, sannan a watan Fabrairun 2013 ta hade da ACN, wani bangare na APGA, da ANPP domin kafa APC don fatattakar PDP daga mulki.

Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da wasu gwamnonin APC, sun ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna.

Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodinma na jihar Imo, wanda ya jagoranci tawagar gwamnonin, ya bayyana cewa sun tafi ne don nuna girmamawa da fatan alheri ga Buhari.

A cikin jawabin da ya yi, Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa wannan ziyarar na daga cikin alamar hadin kai da biyayya da shugabannin APC ke da shi ga Buhari, wanda ya yi shugabanci da amana.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel