2027: Gwamna Ya Yi Gaban Kansa, Ya Kaddamar da Yakin Neman Sake Zaben Tinubu

2027: Gwamna Ya Yi Gaban Kansa, Ya Kaddamar da Yakin Neman Sake Zaben Tinubu

  • Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya karɓi 'dan majalisar dokokin jihar da ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC
  • Okpebholo ya kuma ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027
  • Gwamnan ya bayyana su a jihar Edo sun shiryawa babban zaɓen shekarar 2027 da ake tunkara nan da shekara biyu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a Shekarar 2027.

Mai girma Gwamna Monday Okpebholo ga ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen ne a jihar Edo.

Gwamna Monday Okpebholo
Gwamnan Edo ya kaddamar da yakin neman zaben Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Monday Okpebholo
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Gwamna Monday Okpebholo, ya ƙaddamar da yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisar PDP ya koma APC a Edo

Hakazalika wani ɗan majalisar dokokin jihar daga jam’iyyar hamayya ta PDP, Kaycee Osamwonyi, wanda ke wakiltar Mazabar Uhunmwonde ya sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, shugaba a APC ya fadi tagomashin da Arewa ta samu a mulkin Tinubu

Kaycee Osamwonyi mamba ne a kwamitin kasafin kuɗi na majalisar dokokin jihar Edo.

Gwamna Okpebholo ya karɓi Osamwonyi a fadar gwamnati da ke birnin Benin, bayan da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Jarrett Tenebe, ya gabatar da shi ga gwamnan a hukumance.

Da yake yabawa Osamwonyi da sauran waɗanda suka sauya sheƙa zuwa APC, Okpebholo ya tabbatar da cewa za a ba kowa dama a cikin jam’iyyar.

Ya ƙara da cewa gwamnatinsa na ci gaba da jajircewa wajen aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da suka shafi fannoni daban-daban na tattalin arziƙin jihar, da nufin inganta rayuwar jama’a.

Gwamna Monday Okpebholo
Okpebholo ya kaddamar da yakin neman zaben Tinubu a 2027 Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Twitter

Gwamnan Edo ya ƙaddamar yaƙin neman zaɓen Tinubu

"Muna taya ka murna (Osamwonyi) bisa dawowar ka gida. Dawowar ka ƙari ne ga jam’iyyarmu (APC), tun da yanzu mun samu mutum biyar da suka shigo, kuma hakan ya ƙara mana ƙarfi."
“Mutane da dama daga wasu jam’iyyun siyasa na shirin shigowa jam’iyyarmu. Ina roƙon haɗin gwiwarka don mu samar da ci gaba, kuma tare za mu gina jihar Edo da inganta rayuwar jama’armu.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya tsage gaskiya, ya fadi fargabarsa kan 'yan Boko Haram

"Babban zaɓen da ke gaba, musamman zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027, mun shirya a Edo. Mun riga mun fara yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu tun yanzu.”
“Dole ne mu haɗa kai da matasa a jihar nan, kai ma kana cikin matasa. Ina maka alƙawarin cewa za ka more kasancewarka a cikin jam’iyyarmu, tun da ka yanke shawarar shigowa cikinta.”

- Gwamna Monday Okpebholo

Tinubu ya samu goyon baya a Arewa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar matasan Arewa (ACY) ta nuna goyon bayanta ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa mambobinta za su kaɗa ƙuri'unsu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa suna da mambobi sama da mutum miliyan biyu masu katin zaɓe waɗanda za su iya kaɗa ƙuri'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng