"Mutum 1 Ke Juya APC," Tsohon Mataimakin Shugaban PDP Ya Faɗi Shirin da Suke Yi
- Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Bode George, ya bayyana rashin gamsuwarsa da yadda APC ke tafiyar da harkokin mulki a Najeriya
- A cewarsa, jam’iyyar mai mulki ba ta da ingantaccen tsari na shugabanci da siyasa, kuma mutum daya ne ya ke abin da ya ga dama a cikinta
- Duk da cewa PDP na fuskantar rikice-rikicen cikin gida, jigon ya bayyana kwarin guiwa cewa jam’iyyar za ta magance matsalolinta nan gaba kadan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Cif Bode George, ya soki tsarin APC, tare da bayyana cewa ba ta daingantaccen tsari na siyasa.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan yiwuwar bayyana wata jam’iyya ta uku, kamar SDP da za ta yi tasiri kafin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi

Asali: Twitter
Da yake magana a ranar Laraba a wata hira da aka yi da shi a Channels Television, Cif George ya ce APC na kan tsarin gudanarwar mutum daya kacal.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kan batun samar da sabuwar jam'iyya da za ta yi amo kafin zabe mai zuwa, tsohon mataimakin shugaban ya ce jam'iyya mai kishin kasa ce kawai za ta yi abin arziki.
Jam'iyyar PDP za ta warware rikicinta
Jaridar Vanguard ta ruwaito George ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa za a warware matsalolin da ke cikin jam’iyyar PDP a taron Kwamitin zartarwa na kasa (NEC) na gaba.

Asali: Facebook
A kalamansa:
“Wannan lamari ya fara ne kamar wasa; yanzu kuma ya koma tamkar cutar da ke yaduwa kamar daji. Ya samo asali ne daga yawan son kai na wasu mutane; ba yau abin ya fara ba.”
“PDP na da tsarin da muke amfani da shi wajen warware matsalolinmu. Ranar da muka gudanar da taron NEC mai zuwa, za mu warware matsalarmu. Mutane da dama sun rika fassara dokokin jam’iyyar da kundinta yadda ya dace da ra’ayinsu.”
Jiga-jigan PDP za su tattauna
A cewarsa, taron NEC zai bayar da damar tattaunawa ta gaskiya domin kawo ƙarshen rikicin da jam’iyyar ke fuskanta da fitar da matsaya ta gaba.
Ya ce:
“Na yi imani cewa idan muka haɗu, za mu yi faɗa, mu tattauna mu kuma yi muhawara. A ƙarshe, za mu cimma matsaya ɗaya saboda za mu mayar da hankali kan tsarin da iyayen jam’iyya suka samar tun farko. Wadanda ba su yarda da hakan ba, za su iya barin jam’iyyar su shiga wata.”
Ya ƙara da cewa PDP na sane da waɗanda ke tada jijiyoyin wuya, kuma dole ne ta ɗauki mataki a kansu a taron da za ta gudanar.
Sai dai ya ja kunnen cewa idan PDP ta kasa warware matsalarta a taron NEC na gaba, ta lamari ya gama lalace wa jam'iyyar.
Jam'iyyar PDP ta samu karuwa a majalisa
A wani labarin kuma, kun ji dan majalisar dokokin jihar Enugu, Hon. Eze Gabriel, wanda ke wakiltar mazabar Isi-Uzo karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), ya sauya sheka zuwa PDP.
Hon. Eze, wanda aka zabe shi a 2023 a ƙarƙashin inuwar LP, ya bayyana sauya shekar tasa ne a zaman majalisar dokokin jihar da aka gudanar a ranar Talata, 8 ga watan Afrilu.
Sauya shekar na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar LP ke fuskantar rikicin shugabanci, musamman bayan hukuncin kotun koli da aka yanke.
Asali: Legit.ng