"Ka Yi Hattara da El Rufa'i,' Jagora a APC Ya Shawarci Atiku kan Takarar Shugaban Kasa

"Ka Yi Hattara da El Rufa'i,' Jagora a APC Ya Shawarci Atiku kan Takarar Shugaban Kasa

  • Mataimakin shugaban APC na kasa shiyyar Arewa maso Yamma, Garba Datti, ya roki Atiku Abubakar kan takara a zaben 2027
  • Datti ya shawarci Atiku da kada ya saurari 'yan siyasa irin su Nasir El-Rufai da ke jan hankalin sa wajen samar da kawancen jam'iyyu
  • Ya bayyana cewa akwai alamun cewa tabbas, jam'iyyar adawa ta PDP ba ta da niyyar ba Atiku tutar tsaya mata takarar shugaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaMataimakin shugaban APC na kasa shiyyar Arewa maso Yamma, Garba Datti Muhammad, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da ya cire rai daga sake tsayawa takarar shugaban kasa.

Haka kuma, ya roki tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya daidaita da jam’iyyar APC kuma ya dawo cikinta don a gudu tare, a tsira tare.

Kara karanta wannan

Atiku da shugaban SDP sun ziyarci Aisha Buhari bayan an mata rashi

Atiku
An bukaci Atiku ya hakura da takarar shugaban kasa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Arise News ta ruwaito cewa Garba Datti, ya yi wannan kiran ne a cikin wata budaddiyar wasika da ya aika wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai a Abuja, ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban APC ya shawarci Atiku kan takara

Daily Post ta ruwaito cewa Datti da aka fi sani da Babawo na ganin tun daga shekarar 1993 Atiku ke takarar shugaban kasa, bai dace ba.

Tsohon 'dan majalisar ya na ganin yanzu lokaci ya yi da zai zauna a matsayin dattijo, maimakon cigaba da kashe lokaci da dukiyarsa.

Ya ce Atiku ya dauki darasi daga tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo, wanda ke zaune lafiya a gefe, ya na zama a matsayin dattijo tun bayan barinsa mulki a shekarar 2015.

Atiku
Tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Datti ya ce:

“Yayin da muke kusantar babban zabe mai zuwa, ka sake shiri kamar yadda ka saba. Amma a wannan karon, tun da ka fahimci cewa jam’iyyarka ta PDP ba za ta ba ka tikitin shugaban kasa ba, kana kokarin hada kai da wasu ‘yan siyasa da ba su gamsu da halin da ake ciki ba domin kafa kawance don kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

“Gaskiya Alhaji Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa, shawara ta gare ka cikin gaskiya da tausayi ita ce: don amfanin ka da na ‘yan Najeriya gaba daya, ka hakura da batun tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, lokacin da za ka riga ka cika shekaru 80.”

'Ka yi hankali da El-Rufa'i,' Babawo ga Atiku

Datti ya kuma shawarci Atiku da kada ya saurari wasu ‘yan siyasa kamar Nasir El-Rufai, wadanda ke jan hankalinsa da batun kafa kawance da wasu gabanin 2027.

Tsohon dan majalisar ya kuma bukaci El-Rufai da ya koma APC, domin ya kasance cikin wadanda suka kafa jam’iyyar kuma ya taka rawar gani wajen nasararta.

Ya ce:

“A rubuce yake cewa kai (El-Rufai) kana daga cikin wadanda suka kafa jam’iyyar APC. Bayan ka yi aiki tukuru don ganin nasararta kuma ka yi gwamna a karkashin tutarta har na tsawon shekaru takwas, abin takaici ne ace yanzu ka bar jam’iyyar a wannan lokaci mai muhimmanci.”

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

Nyesom Wike ya caccaki Atiku Abubakar

A baya, kun samu labarin cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya yi martani mai zafi kan kalaman tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Mai taimaka wa Wike, Lere Olayinka ya bayyana cewa ubangidansa, Wike, zai tabbatar da cewa Atiku Abubakar ba zai yi nasara ba a takarar shugaban ƙasa ta 2027 da ke tunkarowa.

Lere ya tabbayar da cewa Wike da mukarrabansa suna yin aiki tukuru domin tabbatar da cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta yi nasara a a babban zaben da ke tafe, ba PDP ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng