Buba Galadima: 'An So Rufe Sanusi II a Abuja, a Saka Dokar Ta Baci a Kano'

Buba Galadima: 'An So Rufe Sanusi II a Abuja, a Saka Dokar Ta Baci a Kano'

  • Buba Galadima, babba a NNPP ya zargi wasu da ƙulla makircin tayar da zaune tsaye a Kano domin a tilasta gwamnatin tarayya ta ayyana dokar ta-baci
  • Ya ce an shirya hakan ba tare da sanin Bola Tinubu ba, inda aka tsara damƙe Muhammadu Sanusi II, a ayyana cewa babu mai rike da sarautar Kano
  • Buba ya ce an yi wani taro a Abuja, inda aka tura wanda ake shirin nadawa Sarkin Kano zuwa Umrah a Saudiyya don kada ya kasance a cikin rikicin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Fitaccen jigo a jam’iyyar NNPP, Alhaji Buba Galadima, ya zargi wasu da yunkurin kawo rudani a jihar Kano don ƙirƙirar dalilin ayyana dokar ta-baci a jihar.

Ya ce makircin ya haɗa da nufin kai wa gwamnatin Kano da masarautar jihar hari ta hanyar ɗaukar matakan hana zaman lafiya, domin a ƙirƙiri dalilin ayyana dokar ta-baci.

Kara karanta wannan

Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers

Buba Galadima
Buba Galadima ya ce an so saka dokar ta baci a Kano. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Asali: Facebook

Buba Galadima ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin siyasa da ake nunawa a tashar AIT, ya ce an shirya komai ba tare da sanin shugaban Bola Tinubu ba. .

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarautar Kano: Maganar shirya taro a Abuja

Injiniya Buba ya ce an yi wani taro a Abuja domin haddasa rikicin siyasa da zai hana zaman lafiya a jihar Kano.

'Dan siyasar ya ce:

“Tinubu bai san abin da ya faru ba, zan iya rantsewa da hakan. An shirya tsaf domin a jefa Kano cikin rudani, a ƙirƙiri dalilin da zai sa a ayyana dokar ta-baci.”

Ya ƙara da cewa a yayin taron aka yanke shawarar tura wanda ake shirin nada sarki zuwa Umrah domin ya nesanta kansa daga yanayin rikicin da ake shirin tayarwa.

Buba Galadima ya ce an so rufe Sanusi II a Abuja

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya fadi hanyar kawo karshen kisan gilla a jihar Filato

A cewar Buba Galadima, waɗanda ke shirya makircin sun yi niyyar gayyatar sarki Muhammadu Sanusi II Abuja sannan su tsare shi.

Sanusi
Yan sanda sun janye gayyatar Sanusi II. Hoto: Masarautar Kano
Asali: Facebook

Ya kara da cewa an shirya cewa dakarun soji za su kasance cikin shiri kuma a bayyana kujerar sarauta a matsayin wacce babu mai ita idan aka rufe Sanusi II.

Ya ce:

“Da zarar an gayyato sarki yau( Ranar Talata), ana sa ran za a tsare shi a Abuja, sannan sojoji su shiga shiri, a ce babu mai kujerar sarautar jihar.”

Sai dai ya ƙi bayyana sunan wanda ake shirin naɗa wa sarkin, yana mai cewa:

“Ku bincika ku gani, duk ƙasar nan ta san abin da ke faruwa.”

Duk da Buba Galadima bai bayyana wanda ya tafi Umra ba, Masarautar Kano ta wallafa a X cewa mai martaba Aminu Ado Bayero ya tafi Saudi Arabia.

Sanarwar ta ce:

"Daga Kasar Saudiya, yayinda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero CFR, CNOL, JP ya fara gudanar da aikin Umrah.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tsoma baki a rikicin sarautar Kano bayan janye gayyatar Sanusi II

"Allah ya kar6i ibada ya tsawaita zamani. Ran Sarki ya dade."

Maganar Peter Obi kan rikicin sarautar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa jagora a jam'iyyar LP, Peter Obi ya yi magana kan gayyatar da rundunar 'yan sanda ta yi wa mai martaba Muhammadu Sanusi II.

Peter Obi ya ce 'yan sanda sun yi abin da ya kamata wajen janye kiran Sanusi II Abuja domin amsa tambayoyi.

Baya ga haka, Obi ya bukaci rundunar 'yan sanda ta rika barin jami'anta a jihohi suna magance irin matsalolin ba tare da zuwa Abuja ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng