Wata Sabuwa: Ana Barazanar Kwace Kujerar Sanatan APC kan Sanata Natasha
- Kungiyar AEISCID ta yi gargadi mai zafi ga Sanata Onyekachi Nwebonyi bisa kalamansa a rikicin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- Shugaban AEISCID, Paschal Oluchukwu, ya soki yadda Onyekachi ke kare Sanata Godswill Akpabio ta hanyar cin mutuncin manyan mutane
- Kungiyar ta bukaci ‘yan mazabar Ebonyi ta Arewa da su fara shirin yi wa Onyekachi kiranye, tana zargin ya zubar da mutuncin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar ‘yan asalin Ebonyi mazauna ketare (AEISCID) ta yi barazana ga Sanata Onyekachi Nwebonyi, mai wakiltar mazabar Ebonyi ta Arewa a majalisar dattawa.
AEISCID ta yi barazanar hada kan 'yan mazabar Ebonyi ta Arewa domin shigar da korafi ga hukumar INEC domin ta kwace kujerar sanatan.

Asali: Twitter
Kungiya ta gargadi sanata kan rikicin Natasha
Gargadin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Paschal Oluchukwu, ya fitar a ranar Talata a birnin Abuja, kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyar ta gargadi Sanata Onyekachi kan kalamai da ɗabi’unsa na baya-bayan nan game da rikicin da ke tsakanin shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Paschal Oluchukwu ya bayyana halayen sanatan a matsayin “rashin kamun kai, rashin ladabi kuma kalaman da ba su dace da matsayin ɗan majalisa ba.”
Ya soki yadda Sanata Onyekachi ke yawan shiga kafafen watsa labarai da cin mutuncin mutanen da ke neman a binciki zargin yunkurin lalata da Sanata Natasha ta yi wa Akpabio.
Kungiya ta nuna damuwa kan halayen sanatan
Shugaban kungiyar ya ce yadda Onyekachi ke kare Akpabio yana nuna cewa bai fahimci rawar da ya kamata ɗan majalisa ya taka ba.
“Muna kallo, karantawa da sauraron munanan kalaman ɗaya daga cikin ’ya’yan mu, Sanata Onyekachi Nwebonyi, wannan abin damuwa ne kwarai,” in ji sanarwar.
Jaridar Tribune ta rahoto sanarwar AEISCID ta kara da cewa:
“Abin takaici da kunya ne yadda wani sanata da ake ganin kamili ne zai rika cin mutuncin manyan Najeriya da suka hada da Dr Oby Ezekwesili da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, don kawai ya kare shugaban majalisa.”

Kara karanta wannan
INEC ta sanar da shugaban Majalisa matakin da ta ɗauka kan buƙatar tsige Sanata Natasha
"Ya zubar da mutuncin jihar Ebonyi" - AEISCID
Kungiyar ta ce da farko ba ta da niyyar magana kan lamarin, amma dole ta sa su yin martani saboda yadda Onyekachi ke ci gaba da furta kalaman da ke bata wa al’ummar Ebonyi suna.
“Ya nuna halaye da suka zubar masa da mutunci kuma suka bata wa mutanen Ebonyi suna gaba ɗaya,” in ji sanarwar.
Kungiyar AEISCID ta zargi Onyekachi da barin aikinsa na majalisa, tana zargin cewa ya koma “mai rike jakar wani ɗan majalisa” wanda shi ma bai fi shi ba sai da mukami kawai.
Kungiyar ta tambaya:
“Me aka yi wa Onyekachi alkawari ne ko me aka ba shi har ya mayar da kansa tamkar karen farauta, tare da barar da mutuncin Ebonyi gaba ɗaya?
“Kiran sunayen mutane yana cin mutuncinsu, da dagewa kan kare wani dan siyasa, da farmakar waɗanda ke neman adalci kan dakatar da Sanata Natasha, abin kunya ne."

Kara karanta wannan
'Ka gaggauta daukar mataki': An fadawa Tinubu abubuwa 2 da ke barazana ga Najeriya
Ana zargin APC za ta ba sanata tikitin gwamna

Asali: Twitter
Kungiyar ta ƙara da cewa akwai rade-radin cewa an kulla wata yarjejeniya ta siyasa dangane da zaɓen gwamnan Ebonyi a 2027.
A cewar kungiyar, ana zargin jam’iyya mai mulki ta yi wa Onyekachi alkawarin maye gurbin Gwamna Francis Nwifuru a 2027, abin da kungiyar ta yi Allah-wadai da shi.
Paschal Oluchukwu ya ce:
“Jihar Ebonyi ba za ta cigaba da kasancewa a hannun mafi munin shugabanni ba, ko da kuwa a ƙarƙashin tsarin rabon mulki ne.
"A bisa halayen da ya nuna a majalisar dattawa ta 10, Sanata Nwebonyi ya riga ya barar da cancantarsa, ya zubar da mutuncinsa."
A ƙarshe, kungiyar ta bukaci al’ummar Ebonyi North su fara shirin tsige Sanata Nwebonyi idan ya ci gaba da irin wannan abin kunyar da take kira da “barar da mutunci.”
INEC ta yi watsi da yi wa Sanata Natasha kiranye

Kara karanta wannan
Sanata: "Akpabio ya buɗe kofar kashe Natasha, kuma ba za a iya cire ta a majalisa ba"
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar INEC ta bayyana cewa ba a cika sharudda a ƙoƙarin tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ba.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar 3 ga Afrilu, 2025, INEC ta ce ta kammala tantance sunayen mutanen da suka nemi tsige sanatar daga majalisa.
Sai dai hukumar ta ce yawan waɗanda suka sanya hannu bai kai adadin da ake buƙata a ƙarƙashin sashe na 69(a) na kundin tsarin mulkin Najeriya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng