Bayan Hukuncin Kotu, Kwankwaso Ya Samu Gagarumar Goyon Baya a NNPP
- Shugabannin jam’iyyar NNPP daga Arewa maso Gabas sun sake tabbatar da cewa suna nan kan goyon bayan Dr. Rabiu Musa Kwankwaso
- Haka kuma sun amince da shugabancin Dr. Ajuji Ahmed a matsayin shugaban jam’iyyar da hukumar zaɓe ta INEC ta amince da shi
- Jam’iyyar ta ce Kwankwaso na samun ƙarin goyon baya daga jama’a a Arewa maso Gabas, kuma za ta ci gaba da tafiya gaba da manufa ɗaya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – NNPP ta bayyana rashin jin daɗinta kan yadda wadanda aka kora daga jam’iyyar, ke ƙoƙarin karkatar da hukuncin babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hanyar yada bayanan karya.
A cewar shugabancin jam’iyyar na yankin Arewa maso Gabas, mutanen da aka kora suna kokarin yaudarar ‘yan NNPP.

Asali: Twitter
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa NNPP na yankin Arewa maso Gabas ta kuma zargi waɗanda aka kora da ƙoƙarin karkatar da fahimtar jama’a domin biyan bukatunsu na kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPP Arewa maso Gabas na tare da Kwankwaso
Yankin Arewa maso Gabas mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin, Hon. Sabo Imam Gashuwa ya sake tabbatar da sahihancin shugabancin Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce:
“A bisa tanadin sashe na 222(1)(a) na kundin tsarin mulki na 1999 da kuma sashe na 81 da 83 na dokar zaɓe ta 2022, kawai bayanan da aka gabatar da su yadda ya kamata a gaban INEC ne ake ɗauka da muhimmanci.
"Sunaye da ayyukan waɗanda aka kora ba su cikin bayanan da INEC ke da su, kamar yadda kotu ta tabbatar.”
Hon. Sabo Gashuwa ya kuma yi kira ga dukkan 'yan jam’iyyar NNPP a Arewa maso Gabas da su ci gaba da zama masu da’a, haɗin kai da kuma tsayawa tsayin daka.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Yankinmu na ci gaba da ƙarfafa kuma na samun goyon bayan jama’a, kuma ba za mu yarda da wani abu da zai karkatar da mu ko ɓatacciyar manufa ba da aka ɗauki nauyin yadawa don dakile cigabanmu.”
NNPP ta nemi hadin kan ‘yan jam’iyya
Shugabancin yankin Arewa maso Gabas na NNPP ya kuma ba wa dimbin magoya bayan jam’iyyar tabbacin cewa NNPP tana daɗa ƙarfafa da zama a ƙarƙashin shugabanci ɗaya.
Ya bukaci jama’a da su yi watsi da dabarun waɗanda aka kora daga jam’iyyar, su kuma ci gaba da marawa jam’iyyar baya domin samun Najeriya mafi inganci.
Hon. Gashuwa ya ce:
“Mun sake jaddada cikakkiyar biyayyarmu da amincinmu ga jagoranmu na ƙasa, Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, wanda hangen nesansa da jajircewarsa ke ci gaba da jagorantar NNPP a faɗin ƙasar nan.
Haka kuma muna da cikakken goyon baya ga shugaban jam’iyya na ƙasa, Dr. Ajuji Ahmed, wanda INEC ta tantance, tare da bin kundin tsarin mulkin jam’iyya.”

Kara karanta wannan
2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1
“Muna goyon bayan sanarwar da sakatariyar NNPP ta ƙasa ta fitar a ranar 3 ga Afrilu 2025 dangane da hukuncin kotun babban birnin tarayya (FCT).
An shawarci Kwankwaso kan hadaka da Atiku
A baya, mun wallafa cewa wani jigo a NNPP, Asiwaju Moshood Shittu, ya yi gargadi ga Rabi'u Musa Kwankwaso da kada ya gaggauta shiga haɗakar jam’iyyun adawa ba tare da cikakken tsari ba.
Asiwaju Shittu ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai, ya nuna damuwa kan yunkurin da ake yi na haɗa kai tsakanin wasu manyan jam’iyyun adawa.
A cewarsa, akwai buƙatar a yi taka-tsantsan wajen shirin kowacce irin haɗaka, domin kaucewa irin kuskuren da aka tafka a shekarar 2014, lokacin da aka kawar da gwamnati mai ci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng