Gwamnonin APC Sun Ziyarci Buhari yayin da ake Rubibin Sauya Sheka zuwa SDP

Gwamnonin APC Sun Ziyarci Buhari yayin da ake Rubibin Sauya Sheka zuwa SDP

  • Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe tare da wasu gwamnoni na APC sun kai ziyarar gaisuwar Sallah ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Rahoto ya nuna cewa ziyarar ta gudana ne karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodinma na jihar Imo
  • Gwamna Uzodinma ya ce ziyarar na nuni da girmamawa, biyayya da kuma goyon bayan da jam’iyyar ke ci gaba da bai wa tsohon shugaban kasar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, tare da wasu gwamnonin jam’iyyar APC sun kai ziyara ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin sun ziyarci Buhari ne a gidansa da ya koma a jihar Kaduna.

Gwamnoni
Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari a Kaduna. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli ne ya wallafa yadda ziyarar ta gudana a wani sako da ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Bayan Dusten Tanshi, Pantami ya sanar da rasuwar babban malamin Musulunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodinma na jihar Imo ne ya jagoranci tawagar, inda suka gaishe da Buhari biyo bayan kammala azumin Ramadan.

A cewar Gwamna Uzodinma, sun je ne don nuna girmamawa da fatan alheri ga Buhari, tare da taya shi murnar kammala azumi lafiya da komawa Kaduna da zama.

APC na girmama Buhari inji Uzodinma

Hope Uzodinma ya bayyana cewa ziyarar ta nuna irin hadin kai da biyayya da shugabannin jam’iyyar ke da shi ga jagoran da ya rike Najeriya cikin gaskiya da rikon amana.

Gwamnan ya ce:

“Ziyarar da muka kai ba wai ta gaisuwar Sallah kadai ba ba ce, alamar girmamawa ce da kuma tunawa da kokarin da Buhari ya yi wajen tabbatar da shugabanci nagari a lokacinsa.”

Jerin gwamnonin da suka halarci ziyarar

Baya ga Gwamna Inuwa Yahaya da Uzodinma, sauran gwamnoni da suka kasance cikin tawagar sun hada da na jihohin Kaduna, Kwara, Nasarawa, Ebonyi, Kebbi, Edo, Kogi, Ondo, Ekiti da Benue.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

Sauran manyan da suka halarta sun hada da mataimakin gwamnan jihar Jigawa da Ministan Tsare-tsare da Kasafin Kudi, tare da wasu manyan jami’an gwamnati da na jam’iyya.

Gwamnoni
Gwamnonin APC tare da Buhari a gidansa na Kaduna. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

Martanin Buhari kan ziyarar gwamnoni

Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi tawagar da hannu bibbiyu, ya nuna godiya da jin dadinsa game da ziyarar gwamnoni da manyan kusoshin jam’iyyar APC.

Ana ganin ziyarar ta kara tabbatar da ci gaba da girmama tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da APC ke yi yayin da wasu 'yan jam'iyyar suka sauya sheka.

Maganar SDP kan sauya shekar Atiku, Obi

A wani rahoton, kun ji cewa jigo a jam'iyyar SDP kuma wanda ya mata takarar shugaban kasa a zaben 2023 ya ce akwai manyan 'yan siyasa da za su shiga tafiyarsu.

Adewole Adebayo ya nuna daga cikin manyan 'yan siyasar akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi.

Dama dai an dade ana rade radin cewa za su koma SDP tun bayan da aka ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya koma jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng