'Dalilai da Ka Iya Sa Tinubu Ya Sauya Kashim a Muƙamin Mataimaki a Zaben 2027'
- Wani kusa a PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya gargadi Bola Tinubu da ka da ya sauya Mataimakinsa, Kashim Shettima, domin hakan zai haifar da rikici a APC
- Akinniyi ya ce Tinubu na iya sauya Shettima domin neman goyon bayan Kiristocin Arewa da yankin Arewa ta Tsakiya kafin zaben 2027
- Akinniyi ya shawarci jam'iyyun adawa da su hada kai, su yi amfani da rabuwar APC domin fitar da Tinubu daga mulki a 2027
- Sai dai APC ta musanta rade-radin sauya Shettima, tana cewa Tinubu bai yanke shawarar sake tsayawa takara ba ko sauya mataimaki ba tukuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Wani kusa a PDP, Dare Glintstone Akinniyi ya yi magana kan jita-jitar sauya Kashim Shettima daga mukaminsa.
Akinniyi ya gargadi shugaban kasa Bola Tinubu ka da ya sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, yana mai cewa hakan zai iya janyo rikici.

Asali: Facebook
'Matsalar da Tinubu zai fuskanta kan sauya Shettima'
A wata hira da Legit.ng ranar Lahadi, Akinniyi ya ce Tinubu zai iya sauya Shettima domin samun goyon bayan Kiristocin Arewa da Arewa ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin matasan PDP ya ce sauya Shettima zai nuna cewa Bola Tinubu yana cikin rudani, kuma hakan zai iya janyo sabbin matsaloli.
Akinniyi ya ce:
"Tinubu zai iya sauya Shettima don ya samu Kiristocin Arewa, amma hakan zai kara wa APC matsala kuma zai cutar da Tinubu."
Akinniyi ya bayyana cewa hanyar da ta fi dacewa ita ce Tinubu ya ci gaba da Shettima don kauce wa faduwa mai muni a zaben 2027.
Yayin da PDP ke sukar tsarin rabon mukamai na APC, inda Akinniyi ya ce mafi kyawun tikitin zabe shi ne Arewa maso Gabas da Kudu maso Gabas.
Akinniyi ya shawarci jam’iyyun adawa da su hada karfi da karfe domin fitar da Tinubu daga mulki, ganin rabuwar kai a cikin jam’iyyar APC.
A hirar, Akinniyi ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya kamata ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a 2027.
Ya bukaci Atiku da ya hada kai da Peter Obi, Nasir El-Rufai da sauran shugabannin siyasa domin fitar da APC daga gwamnati.

Asali: Facebook
Legit Hausa ta tattauna da matashin APC
Ado Mohammed da ke kungiyar goyon bayan Kashim Shettima a Gombe ya yi martani kan jita-jitar da ake yaɗawa.
Ado ya ce babu wani batun shirin sauya Shettima kawai masu neman ta da rigima da gindin zama ne ke ta yadawa.
"Yanzu kam komai ya wuce tun da APC ta ƙaryata masu neman yada karya kan shirin sauya Shettima da wani a Arewacin Najeriya.'
- Cewar matashin
2027: APC ta musanta shirin sauya Shettima
A baya, kun ji cewa jam’iyyar APC ta karyata jita-jitar shirin sauya Shettima, tana mai cewa labarin ba shi da tushe ko makama.

Kara karanta wannan
An bar kasa ba kowa: Shettima ya shilla kasar waje bayan Tinubu ya kwana a Faransa
Daraktan yada labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce babu wata matsala tsakanin shugaban kasa Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima.
Shugabannin Arewa ta Tsakiya suna bukatar shugaban kasa ko mataimaki tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a shekarar 1999.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng