Zaben 2027: Ministan Tinubu Ya Fadi Dalilin Hakura da Yin Takara da Gwamna Radda
- Ministan gidaje da ci gaban birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa ba zai sake tsayawa takara ba da Gwamna Dikko Umaru Radda
- Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa gwamnan ya gudanar da ayyukan alheri da za su sanya ya sake lashe kujerarsa a zaben 2027
- Ministan tarayyan ya yabi Gwamna Radda kan yadda ya kawo ci gaba sosai a cikin shekara biyu da ya yi a ofis a jihar Katsina
- Sai dai, duk da haka ministan gidajen na gwamnatin Bola Tinubu bai cire rai ba wajen jaraba sa'arsa a zaɓen shekarar 2031
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan gidaje da ci gaban birane, Ahmed Dangiwa, ya bayyana cewa ba zai yi takara da gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, a zaɓen 2027 ba.
Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa Gwamna Dikko Radda ya cancanci samun wa’adi na biyu a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Dangiwa ya bayyanawa jaridar The Nation a birnin Abuja cewa Gwamna Radda ya cika alƙawuran da ya ɗauka, don haka ya cancanci sake tsayawa takara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan Tinubu ya yabi Gwamna Radda
Ahmed Dangiwa ya bayyana cewa gwamnan ya gudanar da ayyukan ci gaba a dukkanin ƙananan hukumomin jihar Katsina.
"Zan iya tabbatar muku cewa duk alƙawuran da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabe, ya riga ya cika su cikin shekaru biyu da ya yi a ofis."
“Idan ka zagaya faɗin jihar, za ka ga ayyukan gine-gine suna gudana a dukkan mazaɓu 361 na jihar. Idan zai iya taɓo dukkan mazabu 361 a cikin wannan ɗan ƙanƙanin lokaci, to babu yadda za a yi talaka ba zai ji tasirin gwamnati ba."
"Da irin ayyukan ci gaba da yake yi, babu wani abu da zai hana shi komawa ofis karo na biyu."
"Yana ƙoƙarin ganin jihar ta samu cikakken tsaro tare da kawar da ƴan ta'adda. Haka kuma ya ƙirƙiro rundunar tsaro ta al'umma domin taimakawa tsarin tsaro."

Kara karanta wannan
Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi ya fada kan rashin lafiya da mutuwa kafin ya Cika
“Idan ka duba daga dukkan fannonin tsaro, lafiya, ƙarfafa matasa, da ci gaban tattalin arziƙi, ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa."
- Ahmed Dangiwa
Ahmed Dangiwa ba zai yi takara da Radda ba
Ministan wanda ya sha kaye a zaɓen fidda gwanin gwamna na APC a zaɓen 2023 inda ya zo na huɗu, ya bayyana cewa ba zai ƙara yin takara da Gwamna Radda ba a 2027.
"Ba zan taɓa tsayawa takara da Dikko ba. Idan shekarar 2031 ta zo kuma Allah Ya ƙaddara zan yi takara, to zan yi."
- Ahmed Dangiwa
Gwamna Radda ya sha alwashi kan masarautu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nuna muhimmancin da masarautun jihar suke da su.
Gwamna Radda ya sha alwashin kare martaba, ƙima da mutuncin masarautun jihar Katsina masu daɗaɗɗen tarihi.
Dikko Radda ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen bikin al'ada na Hawan Magajiya da aka gudanar a masarautar Daura.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng