Abin da Sanata Natasha Ta Ce da INEC Ta Yanke Hukunci kan Bukatar Kwace Kujerarta
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi martani bayan hukumar INEC ta yi watsi da ƙorafin da aka gabatar na yi mata kiranye daga majalisa
- Hukumar zaɓe ta kasa ta ce sa hannun mutane 208,132 kacal aka samu, wanda bai kai kaso 50%+1 na 'yan mazabarta da ake bukata a doka ba
- Natasha ta gode wa mijinta, tawagarta, da jama'ar Kogi ta Tsakiya bisa goyon bayansu, sannan ta ce akwai sauran yaƙe-yaƙe biyu a gaba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, 'yar majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya da ke jihar Kogi, ta yi martani kan hukuncin INEC.
A ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025, Legit Hausa ta rahoto cewa INEC ta ce bukatar da aka gabatar na yi wa Sanata Natasha kiranye ba ta cika ka'ida ba.

Kara karanta wannan
INEC ta sanar da shugaban Majalisa matakin da ta ɗauka kan buƙatar tsige Sanata Natasha

Asali: Facebook
Hukuncin da INEC ta yanke kan Sanata Natasha
Da hukumar ke karin bayani a shafinta na X ta bakin kwamishinta kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama'a na kasa, Sam Olumekun, INEC ta ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Jimillar masu rajistar zaɓe a mazabar sanatan Kogi ta Tsakiya ita ce 474,554. Fiye da rabin wannan adadi (wato 50%+1) zai kama 237,277+1, wanda aƙalla ya kai mutane 237,278.
"A cikin runfunan zaɓe 902 da ke cikin gundumomi 57 na rajista da ƙananan hukumomi biyar da ke cikin mazabar, hukumar zaɓe ta tabbatar da cewa daga cikin takardar buƙatar kiranye da masu ƙorafi suka gabatar, an samu sa hannun/dangwalen yatsa 208,132.
"Wannan ya zama kaso 43.86% na masu rajistar zaɓe, wanda ya gaza cika ƙa'idar kundin tsarin mulki da tazarar sa hannun mutane 29,146.
"Saboda haka, wannan buƙata ba ta cika sharuddan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin ƙasa ba. Don haka, ba za a ɗauki wani mataki kan kiranyen Sanatar ba."

Kara karanta wannan
Kurunƙus: Hukumar INEC ta gama nazarin bukatar tsige Sanata Natasha, ta yi hukunci
Sanata Natasha ta yi martani ga hukuncin INEC
Awanni biyu da sanarwar INEC, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi martani, tana mai cewa wannan babbar nasara ce gare ta, 'yan mazabarta, da al'ummar Najeriya.
'Yar majalisar dattawan, ta mika godiya ga mijinta, tawagar masu goya mata baya, al'ummar Kogi ta Tsakiya da al'ummar Najeriya, kan goyon bayan da suka nuna mata.
Hakazalika, Sanata Natasha ta jinjinawa INEC kan wannan namijin kokarin da ta yi na ganin rashin cancantar bukatar da aka gabatar mata na yi mata kiranye daga majalisa.
"Yaƙi 1 ya ƙare, saura 2" - Natasha

Asali: Facebook
To sai dai kuma, 'yar majalisar dattawar, ta ce wannan hukuncin, shi ne fadan farko da aka kawo karshensa, inda ta ce akwai sauran wasu yakokin guda biyu da ke gabanta.
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, Sanata Natasha ta ce:
"Nasara ga al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan
'Ka gaggauta daukar mataki': An fadawa Tinubu abubuwa 2 da ke barazana ga Najeriya
"Yaƙi ɗaya ya ƙare, saura biyu.
"Ina miƙa godiya ta musamman ga ƙaunataccen mijina, tawagar masu goyon baya na, mutanen Kogi ta Tsakiya, da daukacin 'yan Najeriya."
@inecnigeria, kun yi abin a yaba."
George ya gargadi Tinubu kan rigimar Natasha
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban PDP, Bode George ya gargadi Shugaba Bola Tinubu kan rigimar Sanata Natasha Akpoti da Godswill Akpabio.
Bode George ya ce idan har ba a dauki matakin gaggawa ba, rikicin jihar Rivers da kuma dambarwar Sanata Natasha na iya ruguza dimokuradiyyar Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng