Kwankwaso Ya Yi wa APC Illa ana Ribibin Sallah, 'Yan jam'iyyar Sun Koma NNPP

Kwankwaso Ya Yi wa APC Illa ana Ribibin Sallah, 'Yan jam'iyyar Sun Koma NNPP

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi sababbin 'yan NNPP da suka sauya sheka daga jam’iyyar APC a Doguwa
  • Jagoran na NNPP ya kuma halarci taron Sallar Kwankwasiyya karo na bakwai tare da manyan jiga-jigan jam’iyya
  • Taron ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa Aminu Abdussalam, da sauran 'yan NNPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihhar Kano - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karɓi magoya bayan APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Ana ganin sauya shekar da mutanen suka yi a ranar Talata, 1 ga Afrilu, 2025, na kara tabbatar da ci gaban tasirin NNPP a jihar Kano.

Yan NNPP
Kwankwaso ya karbi 'yan APC da suka koma NNPP. Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taro na daban, Sanata Kwankwaso ya karɓi dubban magoya bayan NNPP yayin bikin Sallar Kwankwasiyya karo na bakwai da aka gudanar a Kano.

Kwankwaso ya karbi 'yan APC zuwa NNPP

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa sauya shekar da wasu jiga-jigan APC suka yi zuwa NNPP wata alama ce ta yadda jam’iyyar ke ci gaba da samun karɓuwa a tsakanin jama’a.

Ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP na maraba da duk masu kishin al’umma da ke son kawo sauyi mai kyau ga Najeriya.

Jagoran NNPP na ƙasa ya kuma bukaci sababbin mambobin su yi aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a matakin jihar da na kasa baki daya.

Taron sallar Kwankwasiyya karo na 7

Bayan karɓar sababbin mambobin NNPP, Sanata Kwankwaso ya halarci bikin Sallar Kwankwasiyya karo na bakwai a Kano, inda manyan jiga-jigan NNPP suka samu zuwa.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan siyasar Najeriya ke rububin sauya jam'iyya gabanin zaben 2027

Bikin na bana ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam, tare da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Jibril S. Falgore.

Sauran manyan kusoshin jam’iyyar da suka halarta sun hada da Shugaban NNPP na kasa, Dr. Ahmad Ajuji, da Shugaban jam’iyyar a jihar Kano, Hon. Hashim Dungurawa, da sauransu.

Karin bayani kan taron Kwankwasiyya

Kwankwaso ya bayyana cewa bikin Sallar Kwankwasiyya na daya daga cikin hanyoyin kara dankon zumunci tsakanin magoya bayan jam’iyyar da kuma jaddada kishin kasa.

'Yan kungiyar mawakan Kwankwasiyya sun nishadantar da mahalarta da wakoki daban daban yayin taron.

Kwankwasiyya
Dandazon jama'a yayin taron bikin sallar Kwankwasiyya a Kano. Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Kwankwaso ya kuma yaba da yadda jama’a suka halarci taron, ya na mai cewa hakan alama ce ta ci gaba da karfin jam’iyyar a Kano da kasa baki daya.

Sanata Kwankwaso ya gode wa duk wanda ya samu damar halartar bikin, ya ce NNPP za ta ci gaba da tabbatar da jin dadin al’umma.

Kara karanta wannan

Kungiyar Izalah ta yi maganar kisan ƴan Arewa a Edo, ta fadi hanyar dakile lamarin

Galadiman Kano, Abbas Sanusi ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa Allah ya yi wa Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi rasuwa bayan fama da jinya da ya yi.

Marigayin ya rike sarauta da dama a masarautar Kano kafin mai martaba Muhammadu Sanusi II ya nada shi matsayin Galadiman Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng