'Babu Abin da za a Fasa,' Sanata Natasha Ta Bijirewa Umarnin Gwamnatin Kogi

'Babu Abin da za a Fasa,' Sanata Natasha Ta Bijirewa Umarnin Gwamnatin Kogi

  • Ofishin yada labaran Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya tabbatar da ziyarar da take shirin kai wa yankin Kogi ta Tsakiya na nan daram
  • Wannan ya biyo bayan labarin da ake yadawa kan cewa ta janye shirin gudanar da bikin Sallah tare da mutanen da suka zabe ta zuwa majalisa
  • An fara yada jita-jitar ne bayan gwamnatin Kogi ta sanar da haramta duk wani taro ko gangami a jihar, saboda abin da ta kira barazanar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kogi Ofishin yada labaran Natasha Akpoti-Uduaghan ya ce ziyarar Sanatar take shirin kai wa yankin Kogi ta Tsakiya domin bikin Sallah karama na nan kamar yadda aka tsara.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, tawagar yada labaranta ta karyata rade-radin da ke cewa an soke wannan ziyara.

Kara karanta wannan

Yunkurin raba Sanata Natasha da kujerarta: An ji abin da INEC za ta yi a kwana 90

Natasha
Sanata ta karyata rahoton cewa ta fasa zuwa gida Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo/Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa ofishin yada labaran ya ce bai fitar da wata sanarwa game da soke ziyarar ba, don haka jama’a su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha za ta ziyarci jihar Kogi

Jaridar Punch ta ruwaito cewa ofishin yada labaran Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ya musanta labaran da ake yadawa a kafafen sada zumunta.

Ya kara da cewa:

"Mu na farin cikin tabbatar da cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za ta kai ziyarar gaisuwar Sallah ga al’ummar yankin Kogi Central kamar yadda aka tsara."
"Duk da jita-jitar da ake yadawa a yanar gizo, babu wata sanarwa daga ofishinmu da ke nuna an soke wannan ziyara."

Natasha za ta gana da mutanenta

Sanata Akpoti-Uduaghan ta jaddada kudirinta na yin hulɗa da mutanen da take wakilta da kuma karfafa hadin kai a yankin.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Kamar yadda ta saba, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan tana da niyyar ci gaba da hulɗa da al’ummarta tare da karfafa zumunci da hadin kai a cikin yankin Kogi ta Tsakiya."

Kara karanta wannan

Hanyoyi 4 na bibiyar hakkin Hausawan da aka kashe a jihar Edo," HRN

Natasha
Sanatar Kogi ta Tsakiya Hoto: Natasha H Akpoti
Asali: Facebook

Ofishin ya kuma tabbatar da cewa duk shirye-shiryen da suka dace an kammala su don tabbatar da cewa bikin Sallar zai gudana cikin kwanciyar hankali da nishadi.

Ya ce:

"Muna son tabbatar wa jama’a cewa an kammala duk shirye-shiryen da suka dace don tabbatar da wannan biki mai armashi da nasara. Muna maraba da dukkan al’ummar yankin da su zo su taya mu murnar wannan gagarumin lokaci.'

Wannan bayani ya zo ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa gwamnatin jihar Kogi tana kokarin hana Sanata Akpoti-Uduaghan ziyartar al’ummarta.

INEC ta fusata Sanata Natasha

A baya, kun samu labarin cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta caccaki hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa bisa yadda ta karɓi ƙorafin da wasu suka shigar na neman a yi mata kiranye.

A sanarwar da ta fitar, Sanata Natasha ta bayyana cewa hukumar zaben ta kasa ba ta yi abin da ya dace ba wajen yin watsi da ƙorafin da aka mika mata na neman a tsige ta daga majalisar dattawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng