Jam'iyyar LP Ta Samu Koma baya, 'Dan Takarar Gwamna Ya Sauya Sheka zuwa PDP
- Tsohon ɗan takarar gwamna a Enugu, Chief Chijioke Edeoga, ya koma PDP bayan kasancewarsa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023
- Ya bayyana cewa ya yanke shawarar dawowa ne sakamakon jajircewar Gwamna Peter Mbah da irin jagorancin da yake yi a jihar Enugu
- Shugaban PDP a Enugu, Dr. Martin Chukwunweike, ya ce dawowar Edeoga shaida ce ta ci gaban jam’iyyar, yana mai kira ga wasu su dawo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Enugu - Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a jihar Enugu, a zaben 2023, Chief Chijioke Edeoga, ya koma jam’iyyar PDP.
Edeoga, ya taba riƙe muƙamai daban-daban a karkashin PDP, ciki har da kasancewarsa ɗan majalisar wakilai da kwamishinan kananan hukumomi da muhalli.

Asali: Twitter
'Dan takarar gwamnan LP ya koma PDP

Kara karanta wannan
Gwamnan Edo ya gana da Barau kan kisan Hausawa, ya fadi shirinsa kan iyalan mamatan
Yayin sanar da dawowarsa cikin PDP a hedikwatar jam'iyyar a ranar Litinin, Chief Edeoga ya yabawa salon jagorancin Gwamna Peter Mbah, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kafin wannan sauya sheƙa, an ce Chief Edeoga ya gana da shugabannin PDP na jihar Enugu a ranar 31 ga Janairu.
A jiya, Edeoga ya isa helkwatar PDP ta jihar a cikin gagarumin jerin gwanon motocci, inda shugabannin jam’iyyar karkashin jagorancin, Dr. Martins Chukwunweike, suka tarbe shi.
Da yake jawabi ga mambobin jam’iyyar, Edeoga ya godewa Gwamna Mbah da shugabannin PDP na mazabarsa ta Eha-Amufu Ward III, Karamar Hukumar Isi-Uzo, da na jihar baki ɗaya saboda sauƙaƙa komarsa cikin jam’iyyar.
"Wasu ba za su ji dadi ba" - Cif Edeoga
Ya kuma sha alwashin ƙara sadaukar da kansa ga PDP, ya na mai cewa lokaci ya yi da kowa zai haɗa kai da Gwamna Mbah wajen ci gaban jihar Enugu.
“Ina matuƙar yaba wa da hangen nesa, ƙirƙira, da salon jagorancin Gwamna Mbah, wanda ya ƙarfafa min guiwa na dawo PDP."
- Edeoga.
The Nation ta rahoto Edeoga ya amince cewa ba kowa zai yi maraba da dawowarsa PDP ba, amma ya jaddada buƙatar haɗin kai domin gina tafiyar jam'iyyar gabanin zaɓen 2027.
“Na fahimci cewa wasu ba za su yi farin ciki da komawata PDP ba, amma ina ganin lokaci ya yi da za mu haɗa kai a matsayin iyali daya domin gina jam'iyya mai ƙarfi."
- Edeoga.
PDP ta yi maraba da dan takarar gwamnan LP

Asali: Twitter
Shugaban PDP na jihar Enugu, Dr. Martin Chukwunweike, ya tarbi Edeoga da farin ciki, yana mai cewa dawowarsa shaida ce ta kyakkyawan jagorancin Gwamna Mbah.
“Muna farin cikin ganin Edeoga ya dawo cikin PDP, kuma muna da tabbacin cewa ƙarin tsofaffin mambobin da suka bar jam’iyyar za su dawo nan gaba kaɗan."
- Dr. Martin Chukwunweike.
Shugaban Karamar Hukumar Isi-Uzo, Obiora Obegu, ya bayyana dawowar Edeoga a matsayin “mataki mai kyau,” yana mai cewa hakan zai ƙarfafa jam’iyyar PDP ta zama jam'iyya mai karfi ba tare da rikice-rikice ba.
Yadda 'yan siyasa ke sauya sheka gabanin 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Najeriya ta fuskanci gagarumin sauyin jam’iyyu da ya shafi manyan 'yan siyasa, daga Janairu zuwa Maris din 2025.
Wasu manyan 'yan siyasa da suka sauya sheka sun hada da tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, Sanata Ned Nwoko, Sanata Ahmad Babba Kaita da sauransu.
Asali: Legit.ng