'Da Girmanka Kana Karya a Ramadan': An Soki Atiku kan 'Karairayi', an Ja Masa Hadisi
- Hadimin Wike, Lere Olayinka ya musanta ikirarin Atiku Abubakar cewa PDP ta fifita Okowa kan Wike a matsayin mataimakin takarar shugaban kasa na 2023
- Olayinka ya ce Atiku bai girmama watan Ramadan ba saboda ya bayyana abin da ba gaskiya ba game da yadda PDP ta zaɓi ɗan takarar mataimakin shugaban kasa
- Ya yi mamakin yadda Atiku ke cewa an fi zaɓar Okowa, alhali Okowa ya samu ƙuri’u biyu ne, yayin da Wike ya samu ƙuri’u 13 daga kwamitin
- Olayinka ya ce Atiku yana guje wa gaskiya, kuma hakan na iya zama dalilin da ya sa Allah bai karɓi addu’arsa ba, har ya kasa cin zaben shugaban kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Hadimin ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi martani ga tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar.
Lere Olayinka ya musanta ikirarin Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa na PDP kan zaɓen 2023.

Asali: Facebook
Wike ya yi martani ga Atiku Abubakar
Olayinka ya yi martanin ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook domin fayyace gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya biyo bayan Atiku ya ce kwamitin PDP da aka kafa don zaɓar mataimakin shugaban ƙasa bai zabi Wike ba.
A rahoton, Atiku ya ce kwamitin ya fifita tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, kan Nyesom Wike a matsayin zaɓin farko.
Olayinka ya zargi Atiku da rashin girmama watan Ramadan saboda faɗar abin da ba gaskiya ba.
Ya tambaya yaya za a ce mutum mai ƙuri’u biyu ne aka zaɓa kan wanda ke da ƙuri’u 13.
Olayinka ya ce:
"Kwamitin PDP ya zaɓi Wike a matsayin mataimakin Atiku, amma saboda dalilansa, ya fi son Okowa wanda ya samu ƙuri’u biyu kacal, wannan ita ce gaskiyar da ya kamata Atiku ya faɗi."

Kara karanta wannan
"Hantar Tinubu ta kaɗa": An faɗi wanda ya dace Atiku, Obi da El Rufai su marawa baya a 2027
"Al-Bukhari (1903, 6057) ya ruwaito Abu Hurayrah yana cewa Annabi (SAW) ya ce: ‘Duk wanda bai daina yin ƙarya da aikata ta ba, Allah ba ya buƙatar azuminsa.’”
"Abin takaici, Atiku ya zaɓi yin ƙarya a watan Ramadan, wata mai tsarki, yana mantawa da cewa Allah ba ya karɓar addu’ar maƙaryaci."

Asali: Facebook
Zaben 2023: 'Wike bai yi nadama ba' - Hadiminsa
Olayinka ya ce kwata-kwata mai gidansa bai yi nadamar rashin samun muƙamin zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa ba.
Ya kara da cewa:
"Na ce tun farko, Wike ba shi da nadamar rashin zama mataimakin Atiku, kuma bai yi nadamar matsayinsa kan zaɓen shugaban ƙasa ba."
Edo: Atiku ya soki kisan ƴan Arewa
Kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da kisan rashin imani da aka yi wa wasu mafarauta ƴan Arewa a jihar Edo.
Atiku ya bukaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike a bayyane kuma su tabbatar an hukunta masu laifi.
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan waɗanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan al'amarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng