Matsala Ta Tunkaro El Rufai bayan Barin APC, Jam'iyyar SDP Ta Fadi Matsayinsa

Matsala Ta Tunkaro El Rufai bayan Barin APC, Jam'iyyar SDP Ta Fadi Matsayinsa

  • Jam’iyyar SDP ta Kaduna ta bayyana cewa tsohon gwamna Nasir El-Rufai ba mambanta ba ne, duk da ya fice daga APC zuwa SDP
  • El-Rufai ya ce ya fice daga APC ne saboda rashin daidaituwa tsakanin dabi’unsa da shugabancin jam’iyyar, amma SDP ta ce ba a bi ka’ida ba
  • Mataimakin Sakataren SDP na Arewa maso Yamma, Idris Inuwa, ya ce babu wata hujja da ke nuna El-Rufai ya shiga jam’iyyar ta hanyar doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Jam’iyyar SDP reshen jihar Kaduna ta yi magana kan matsayin Nasir El-Rufai bayan ya bar APC mai mulki.

Jam'iyyar ta nesanta kanta daga tsohon Gwamna Nasir El-Rufai, ta na mai cewa ba mambanta ba ne.

SDP ta barranta kanta da Nasir El-Rufai
Jam'iyyar SDP ta ce har yanzu Nasir El-Rufai ba mambanta ba ne. Hoto: @Elrufai.
Asali: Twitter

SDP ta yi magana kan matsayin Nasir El-Rufai

Kara karanta wannan

Siyasa kenan: Bayan kare El Rufai a baya, shugabar matan APC ta dawo caccakarsa

Mataimakin Sakataren SDP na Arewa maso Yamma, Idris Inuwa, ya ce batun shigar El-Rufai cikin jam’iyyar jita-jita ce, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Inuwa ya ce kwata-kwata ba su san da El-Rufai a jam'iyyar ba saboda ba mambanta ba ne har yanzu.

Sakataren jam'iyyar ya shawarci El-Rufai da sauran mutanen da ke son shiga jam’iyyar su bi matakan da suka dace.

Inuwa ya ce:

“Idan ya kasance El-Rufai da wasu sun shiga SDP, ba mu da wata shaida daga Shugaban SDP na Kaduna ta Arewa ko na mazabar Unguwar Sarki."
“Mu na ba da shawara ga kowa da kowa da ke sha’awar shiga jam’iyyar ya bi dokoki da ka’idojin da aka tanada."

Haka kuma, Inuwa ya musanta rushe kwamitin SDP na Kaduna da aka yi, yana mai cewa hakan saba doka ne kuma an yi shi ba tare da bin ka’ida ba.

“Kwamitin zartaswa na jam’iyyar SDP reshen Kaduna bai yarda da rushewar kwamitin ba kamar yadda wata wasika daga hedkwatar jam’iyyar ta bayyana."

Kara karanta wannan

'Tsofaffin ministoci da sanatoci sun shiga SDP don kifar da Tinubu a 2027,' Gabam

- Cewar Inuwa

SDP a jihar Kaduna ta sake jikawa El-Rufai aiki
Jam'iyyar SDP a Kaduna ta barranta kanta da Nasir El-Rufai. Hoto: Nasir El-Rufai.
Asali: Twitter

SDP ta fadi yadda tsarin jam'iyyar yake yi

Idris Inuwa ya kara da cewa kwamitin na jiha ya fito ne daga sahihiyar taron jam’iyya kuma yana da wa’adin shekaru hudu da har yanzu yana aiki.

Ya ce kundin tsarin mulkin jam’iyyar SDP ya bayyana yadda za a rushe kwamitin jiha, wanda dole ne a gudanar da bincike tare da ba da damar kare kai.

A cewarsa:

“Kwamitin Jiha ya samu sahalewar mambobi a taron jam’iyya, kuma yana aiki bisa ka’idojin kundin tsarin mulkin jam’iyyar har wa’adinsa ya cika.”
“Ina so in jaddada cewa tsarin mulkin SDP yana bukatar a gudanar da bincike, a kafa kwamiti, a ba da damar kare kai kafin a dauki mataki."

Ana zargin manyan APC za su bi El-Rufai

Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya sauya sheƙa zuwa SDP saboda rashin daidaito tsakanin manufofin APC da ra'ayinsa.

Ana zargin wasu shugabannin APC da na kusa da Muhammadu Buhari za su iya barin jam'iyyarsu zuwa SDP.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng