An Fara Bugawa kan Kudirin Hana Tinubu, Atiku da Obi Takara a 2027
- Majalisar Wakilai ta amince da kudirin hana masu shekaru sama da 60 yin takarar shugaban kasa da gwamna a jihohi
- PDP da CUPP sun soki kudirin, suna masu cewa matsalolin Najeriya ba na shekaru ba ne, illa cin hanci da rashin iya shugabanci
- Ita SDP ta ce duk da cewa matasa na da muhimmanci a shugabanci, gogewa da kwarewa su ne ke kawo nasara ba shekaru ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyun PDP, SDP da CUPP sun soki matakin da Majalisar Wakilai ke kokarin dauka na hana ‘yan takarar da suka haura shekara 60 yin takarar shugabancin kasa da gwamna.
Majalisar ta amince da kudirin a karatu na biyu a ranar Alhamis, wanda idan aka amince da shi zai hana shugaba Bola Tinubu, Atiku Abubakar da Peter Obi shiga zaben 2027.

Kara karanta wannan
Kariya ta kare: Majalisa ta amince da kudirin da zai tubewa ƴan siyasa zani a kasuwa

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa PDP ta ce kudirin ya nuna rashin fifita kwarewa, ta ce babbar matsalar Najeriya ita ce cin hanci da rashawa, ba shekarun shugabanni ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP: 'Matsalar Najeriya ba shekaru ba ne'
Jam’iyyar PDP ta caccaki ‘yan majalisar wakilai da suka gabatar da kudirin, tana mai cewa hakan na nuna suna mai da hankali kan abubuwa marasa muhimmanci.
Mataimakin shugaban matasan PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce:
"Wannan shi ne zaman majalisa mafi rashin sanin ya kamata da muka taba yi a tarihin Najeriya.”
Timothy Osadolor ya kara da cewa:
"Matsalar da muke da ita ba shekaru ba ne, matsalar ita ce cin hanci da rashawa, rashin iya shugabanci da rashin kishin kasa.
"Maimakon su mayar da hankali kan wadannan matsaloli, sai suka koma kan batun da ba shi da muhimmanci."
Osadolor ya ba da misalai da kasashe kamar Amurka da Singapore, inda shugabanni masu sama da shekara 60 ke jagoranci cikin nasara.
CUPP: 'Ba shekaru ne matsalar Najeriya ba'
Sakataren yada labaran kungiyar CUPP, Mark Adebayo, ya yi watsi da batun cewa shekaru za su iya hana Najeriya ci gaba.
Mark Adebayo ya ce:
"Idan mutum ya na da dabi'a da halin cin hanci da rashawa, ko ya na da shekaru 30 ne ko 60, to zai ci gaba da aikata hakan.”
Adebayo ya kawo misalan tsohon shugaban Amurka Joe Biden da Lee Kuan Yew na Singapore, ya na mai cewa ba shekaru ba ne ke kawo shugabanci nagari, illa mutunci da kwarewa.
"Mun taba samun shugabanni da suka yi kasa da shekaru 50, har ma da wadanda ke kasa da 40, amma me suka yi?
Matsalar Najeriya ba shekaru ba ne, matsalar ita ce rashin iya shugabanci, cin hanci da rashin kishin kasa."
SDP: 'Gogewa da kwarewa ne abin lura'
A nata bangaren, jam’iyyar SDP ta ce duk da cewa matasa na da muhimmanci a shugabanci, gogewa da kwarewa sun fi tasiri wajen cimma nasara.
Sakataren yada labaran SDP, Rufus Aiyenigba, ya ce:
"Mun taba samun matasa a matsayin shugabanni a baya, wasu sun yi kokari, wasu kuma sun gaza."
Ya bayar da shawarar cewa ya kamata a duba ingancin ‘yan takara ta hanyar tilasta musu muhawara kai tsaye.

Asali: Twitter
Akpabio ya ce Kano za ta dawo hannun APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio ya ce APC za ta kwace Kano a 2027.
Sanata Godswill Akpabio ya ce suna da mutane jajirtattu kamar shugaban APC na kasa, Abdulahi Ganduje, Sanata Barau Jibrin da Basheer Lado da za su musu aiki a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng