2027: Akpabio Ya Fadi yadda APC za Ta Kwato Kano, Ta Kawowa Tinubu Nasara

2027: Akpabio Ya Fadi yadda APC za Ta Kwato Kano, Ta Kawowa Tinubu Nasara

  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce APC za ta kwato Kano daga hannun NNPP a 2027
  • Ya ce jagororin APC irin su Dr Abdullahi Ganduje, Sanata Barau Jibrin da Sanata Basheer Lado za su ja ragamar nasarar
  • Akpabio ya kare Sanata Lado daga zargin fitar da sirrin gwamnati a matsayinsa na mai ba shugaban kasa shawara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta karbe Kano a zaben 2027.

Akpabio ya ce APC tana da cikakken shiri tare da jagorancin manyan jiga-jigan jam’iyyar da za su tabbatar da nasararta a Kano.

Akpabio
Akpabio ya ce Kano za ta dawo hannun APC a 2027. Hoto: Nigerian Senate|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Da yake magana a wata tattaunawa da aka yi da shi a ranar Alhamis, Punch ta wallafa cewa Akpabio ya ce kasancewar suna da Abdullahi Ganduje, Barau Lado, APC ta riga ta kwace Kano.

Kara karanta wannan

'Za mu hana Mutfwang tazarce': Minista ya fadi yadda APC za ta kwace Filato a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'APC za ta karbe Kano a 2027' - Akpabio

Shugaban majalisar dattawa ya jaddada cewa APC ta na da cikakken tasiri a Kano, wanda hakan ke nuni da cewa jam’iyyar za ta samu nasara a zaben 2027.

Akpabio ya ce:

“Tun kafin 2027, mun riga mun tabbatar da cewa da Sanata Barau, Dr. Abdullahi Ganduje da kai (Lado), Kano tuni ta dawo hannun APC.”

Akpabio ya bayyana cewa kokarin da Ganduje da Barau ke yi zai taimaka wajen tabbatar da nasarar jam’iyyar a Kano.

Ya ce APC za ta yi aiki tukuru don tabbatar da cewa jihar Kano ta dawo hannun jam’iyyar a zabe mai zuwa.

Ganduje
Shugaban APC, Abdulahi Ganduje. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Akpabio ya wanke Lado daga zargi

Baya ga batun nasarar APC a Kano, Akpabio ya yi magana kan rade-radin cewa ana zargin Sanata Lado da fitar da sirrin gwamnati a matsayinsa na mai ba shugaban kasa shawara.

Kara karanta wannan

Barau: An saki adadi da bayanin tantance matasan da suka nemi tallafin Barau N5m

Ya musanta wadannan zarge-zarge, ya na mai cewa tun bayan hawar Lado a ofis, ba a taba samun wani sirri da ya fita daga majalisa zuwa kafafen yada labarai ba.

A cewar Akpabio:

“Tun bayan shigansa ofis, ba a taba samun wani sirrin gwamnati da ya fita daga majalisa zuwa kafafen yada labarai ko shafukan sada zumunta ba.”

Ya ce irin wannan zargin ba gaskiya ba ne, domin Lado mutum ne mai tsayawa a kan gaskiya da amana.

Sanata Lado ya gode wa Akpabio

Sanata Basheer Lado ya nuna godiyarsa ga Akpabio bisa goyon bayan da yake ba shi da kuma yadda yake tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin majalisar dattawa da bangaren zartaswa.

Vanguard ta wallafa cewa ya ce:

“Kasancewarka a nan ba wai alama ce kawai ta hadin kai tsakanin bangaren zartaswa da majalisa ba, alama ce ta cewa shugabanci na bukatar hadin kai.”

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Lado ya jinjina wa Akpabio bisa rawar da yake takawa wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Bola Tinubu.

Ya ce Akpabio ya kasance jagora mai fahimtar yadda ake tafiyar da mulki, wanda ke tabbatar da kyakkyawar dangantaka tsakanin majalisa da bangaren zartaswa.

Majalisa ta watsar da korafin Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa majalisar dattawa ta yi watsi da korafin da wani dan mazabar Sanata Natasha Akpobi ya shigar.

Majalisa ta yi watsi da korafin ne bayan an yi cacar baki yayin da aka fara tattaunawa da bangaren Sanata Natasha.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng