Faɗan Giwaye: Ɗan Majalisa na Neman Kassara Sanata Yari domin Rage Masa Tasiri?
- 'Dan majalisar wakilai, Aminu Sani Jaji ya nesanta kansa daga wata makarkashiya da ake cewa ana kullawa don rage tasirin Abdulaziz Yari
- Hon. Jaji ya bayyana cewa bai taɓa yin wani abu da zai ci mutuncin Sanata Yari ba, kuma labaran da ke alaƙanta shi da haka ba gaskiya ba ne
- Ya ce wasu ‘yan siyasa da suka rasa tasiri ne ke yaɗa ƙarya domin su haddasa rikici da kuma ɓata sunansa a cikin jam’iyyar APC mai mulkin kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Yayin da rikicin jam’iyyar APC na jihar Zamfara ke kara ƙamari, Hon Aminu Sani Jaji ya yi magana.
'Dan majalisar wakilan daga Zamfara ya nesanta kansa daga wata makarkashiya da ake cewa ana kullawa don rage tasirin Sanata Abdulaziz Yari.

Kara karanta wannan
Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

Source: Facebook
Hon. Jaji ya musanta zargin cin amanar APC
Tribune ta ce Jaji da ke wakiltar mazabar Kaura Namoda/Birnin Magaji, ya fitar da sanarwa inda ya musanta rahotannin da ke danganta shi da cin amanar jam’iyya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan majalisar ya yi fatali da labarin da ake yaɗawa cewa yana daga cikin masu shirya ɓata sunan Yari don rage tasirinsa.
Hon. Jaji ya bayyana wannan rahoto a matsayin “mugun nufi”, ya na mai jaddada cewa ba zai taɓa yin rashin girmamawa ga Yari ko wani jagoran jam’iyyar ba.
Ya lissafo gudunmawarsa ga jam’iyyar APC a Zamfara da ma sakatariyar ƙasa, yana mai cewa ba shi da hannu a kowace irin makarkashiya da za ta cutar da jam’iyyar.
Sanarwar ta ce:
"Hon. Aminu Sani Jaji, dan majalisa mai wakiltar Kaura Namoda/Birnin Magaji a Zamfara ya kaɗu kan wani ƙagaggen labari da ke zarginsa da cin amanar jam’iyya.
"Aminu Sani Jaji ɗan jam’iyyar APC ne na kwarai, kuma bai taɓa ɗaukar matakin da zai cutar da jam’iyya ba.

Kara karanta wannan
Atiku ya tuna baya, ya fadi dalilin kin zabar Wike a matsayin mataimakinsa a 2023
"Hulɗata da Sanata Abdulaziz Yari ta daɗe tun shekaru da dama, kuma babu wani ƙaryar da wata ƙungiya za ta kirkira da zai iya ɓata wannan dangantaka.
"Mu na shawartar waɗanda ke yaɗa waɗannan jita-jita da su daina amfani da sunan Sanata Yari wajen aiwatar da shirinsu na ɓarna."

Source: Twitter
Dan majalisar ya jaddada biyayyarsa ga APC
Hon. Aminu Jaji ya jaddada biyayyarsa ga APC inda ya ce idan ba a manta ba shi ne tsohon Darakta-Janar na kamfen din Tinubu da Kashim a zaben 2023.
Ya kara da cewa:
"Ni tsohon Darakta-Janar ne na Sashen Tuntuɓa da Wayar da Kan Jama’a a kamfen ɗin Tinubu/Shettima na Arewa maso Yamma, kuma ba zan taɓa aiki da masu neman rusa APC ba.
"Muna kuma ƙarfafa wa wanda ke kitsa wannan ƙage da ya fito fili ya bayyana kansa idan yana da gaskiya, maimakon ɓoye wa a bayan wata ƙungiya maras tushe.
Dan majalisar APC ya karbi jiga-jigan adawa
Kun ji cewa dan majalisar wakilai, Hon. Aminu Sani Jaji ya karbi dan takarar gwamna a AAC, Muhammad Kabir-Sani da magoya bayansa.
Jaji ya ce sauya sheƙar waɗanda suka shiga APC zai ƙarfafa jam’iyyar, ya kuma tabbatar musu da adalci da haɗin gwiwa a harkokin siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng