Shirin Kawar da Gwamnatin APC: Sababbin Jam'iyyu na Tururuwar Yin Rajista da INEC

Shirin Kawar da Gwamnatin APC: Sababbin Jam'iyyu na Tururuwar Yin Rajista da INEC

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta sanar da cewa yanzu haka, sababbin jam'iyyu akalla 91 ne ke son a yi masu rajista
  • Sai dai wasu, musamman daga APC na zargin tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a PDP, Atiku Abubakar ne ke daukar nauyi su
  • Amma a bangaren PDP, mataimakin Shugaban matasa, Timothy Osadolor ya danganta hakan da fashin hadin kan ƴan adawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaHukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa ta karɓi buƙatun rajistar sababbin jam’iyyu guda 91.

Buƙatar na zuwa a daidai lokacin da shirin kawar da jam’iyyar APC a zaɓen 2027 ke ƙara karfi, musamman bayan ƙawancen ƴan adawa.

Adawa
Sababbin jam'iyyu na son rajista da INEC Hoto: Cmr Abbansy/Mahmood Yakubu/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa PDP ta ce yawan buƙatun rajistar jam'iyyun ya nuna rashin haɗin kai tsakanin shugabannin jam’iyyun adawa.

Kara karanta wannan

Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin Shugaban Matasa na PDP, Timothy Osadolor, ya bayyana cewa, maimakon kafa jam’iyyu da yawa, kamata ya yi ‘yan adawa su haɗu wuri guda don tunkarar APC.

Jam'iyyar PDP ta fadi dabarar kawar da APC

MSN ta ruwaito cewa Timothy Usodor na ganin abin da ake bukata kawai shi ne samun jam’iyyar adawa mai ƙarfi da za ta kalubalanci mulki tare da ba wa waɗanda za su iya tafiyar da ƙasar damar yin hakan.

Ya ce:

“A ganina, samun buƙatun rajistar jam’iyyu 91 na nufin a ƙarshe INEC na iya amincewa da 40, ko wani adadi da ya dace. Amma tambaya ita ce, shin hakan zai magance matsalarmu?
"A’a, ba zai magance ta ba. Idan haka ne, me ya sa za mu ɓata lokacimu a kai? Don haka, ina ganin babu buƙatarsa kwata-kwata.”

APC ta soki rajistar jam'iyyun da INEC

Da ya ke martani kan masu ƙoƙarin sabuwar rajista, Mai Magana da yawun APC, Bala Ibrahim, ya yi watsi da shirin, yana mai cewa haƙansu ba zai cimma ruwa ba.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Gwamnan APC ya hango damuwa a zaben 2027

Atiku
An zargi Atiku da hannu a cikin sababbin jam'iyyu Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Bala Ibrahim ya yi zargin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na da hannu a ciki, amma hakan ba zai hana APC cin nasara a 2027 ba.

INEC: An gano amfanin rajistar sababbin jam'iyyu

A cewar Mark Adebayo na CUPP, ƙin rajistar sababbin jam’iyyu zai raunana dimokuraɗiyya, yana mai cewa yawan jam'iyyun zai kara wa abubuwa armashi.

Ya ce:

"A ƙasashe irin su Amurka da Birtaniya, akwai daruruwan jam’iyyu, amma kaɗan ne ke yin tasiri. Saboda haka, ƙara jam’iyyu zai ƙarfafa ‘yan adawa."

Ya yi gargaɗin cewa rashin sababbin jam’iyyu na iya bai wa APC damar kafa gwamnati ta jam’iyya guda a Najeriya.

Adebayo ya ce

"Hakkinsu ne duk waɗanda ke son sauyawa daga kungiyoyin siyasa zuwa jam’iyyun siyasa. Ba na ganin akwai wata matsala a cikin hakan, kuma ba barazana ba ce ga kowace ƙungiya ko jam’iyya ta siyasa."

INEC ta karbi shirin kiranyen Natasha

A baya, kun ji cewa INEC ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, game da yunkurin yi mata kiranye daga majalisar dattawa.

Hukumar ta ce ta karɓi cikakkun bayanan masu ƙorafi bayan an gyara kura-kuran da aka samu a takardun da suka shigar tun da farko, kuma za a dauki mataki na gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel