Wike Ya Yi Wa Atiku Martani Mai Zafi, Ya Sha Sabon Alwashi

Wike Ya Yi Wa Atiku Martani Mai Zafi, Ya Sha Sabon Alwashi

  • Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya taso Atiku Abubakar a gaba kan abin da faru a lokacin zaɓen 2023
  • A wani martani da hadiminsa ya yi, ya bayyana cewa Wike bai yi nadamar rashin zama mataimakin Atiku ba a zaɓen da ya wuce
  • Ya bayyana cewa Wike ya taka rawar gani wajen faɗuwar Atiku, kuma zai sake tabbatar da cewa bai yi nasara ba a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Lere Olayinka, mai taimakawa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, kan harkokin yaɗa labarai, ya yi martani kan kalaman Atiku Abubakar.

Lere Olayinka ya jaddada cewa ubangidansa zai tabbatar da cewa Atiku Abubakar, bai yi nasara ba a takarar shugaban ƙasa a 2027.

Wike ya caccaki Atiku
Hadimin Wike ya yi wa Atiku martani Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Lere Olayinka ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Laraba, 26 ga watan Maris 2025.

Kara karanta wannan

Atiku ya tuna baya, ya fadi dalilin kin zabar Wike a matsayin mataimakinsa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku bai yi nadamar daukar Wike takara ba

Hadimin na Wike ya yi magane yayin da yake mayar da martani kan kalaman Atiku, inda ya ce bai yi nadamar rashin ɗaukar Wike a matsayin mataimakinsa ba a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

A lokacin zaɓen, Atiku, wanda ya tsaya takara a ƙarkashin PDP, ya bayyana cewa wani kwamitin jam’iyyar ya gabatar masa da sunayen mutane uku a matsayin waɗanda zai iya yin takara tare da su.

Waɗanda aka zaba sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, Wike, da kuma tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel.

A ƙarshe dai, Atiku ya zabi Okowa a matsayin abokin takararsa, kuma ya ce bai yi nadamar rashin zaɓar Wike.

Atiku ya ce ya ƙi ɗaukar Wike ne saboda sunansa ne na biyu a cikin jerin sunayen mutanen guda uku da aka gabatar masa.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya kawo karshen maganar takararsa a 2027, ya fadi shirinsa

Wane martani Wike ya yi wa Atiku?

A martanin da ya yi, Lere Olayinka ya yi watsi da maganar Atiku, ya na mai cewa Wike bai yi nadamar rashin samun tikitin mataimakin shugaban ƙasa ba.

Ya ƙara da cewa Wike ya taka rawa wajen faɗuwar Atiku a zaɓen 2023, kuma zai tabbatar da cewa hakan ya sake faruwa a 2027.

Atiku da Wike
Atiku Abubakar da Nyesom Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, Atiku Abubakar
Asali: Facebook
"Shekara biyu bayan ya yi sanadiyyar faɗuwar jam’iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa da za ta iya cin nasara, Atiku ya na ba da dalilan da ya sa bai ɗauki Wike a matsayin abokin takararsa ba, yana mai cewa bai yi nadama ba."
"Wani ya gayawa wannan da ya saba yin takarar shugaban ƙasa cewa Wike ma bai yi nadama ba kan tabbatar da cewa ya sha kaye a zaɓen da ya gabata, kuma zai sake tabbatar da cewa ya ci gaba da faɗuwa."

- Lere Olayinka

Wike ya magantu kan sulhu a Rivers

Kara karanta wannan

Yadda Atiku, Peter Obi da El Rufai za su zaɓi wanda zai gwabza da Tinubu a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan yin sulhu da Gwamna Siminalayi Fubara na Rivers.

Wike ya bayyana cewa ba a adawa da yin sulhu ko zaman tattaunawa domin warware rikicin siyasar jihar mai arziƙin mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng