Yan Kwankwasiyya Sun Yi wa Masoyin Atiku Rubdugu kan 'Sauya Shekar' Kwankwaso
- Wani Dr. Usman Isyaku ya gamu da caccakar ƴan Kwankwasiyya biyo bayan kalamansa a kan jagoransu, Rabi'u Musa Kwankwaso
- Usman Isiyaku, saka Kwankwaso a gaba kan dokar ta ɓaci a jihar Ribas tare da zarginsa da yi wa Bola Tinubu aiki ta karkashin ƙasa
- Guda daga cikin ƴan Kwankwasiyya, Dr. Ibrahim Musa, ya na ganin kalaman sa sun fi kama bundum-bundum da rashin makama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani malamin jami’a, Usman Isiyaku, wanda ya taso Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso a gaba, ya gamu da fushin magoya bayan Kwankwasiyya.
Usman Isiyaku ya caccaki Sanata Kwankwaso saboda jinkirin da ya yi wajen bayyana matsayarsa kan dokar ta ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya kafa a jihar Rivers.

Kara karanta wannan
Sanatan Bauchi ya ba mutane kunya da azumi, bidiyosa yana rabon kuɗi ya shiga intanet

Asali: Facebook
Bayan da Kwankwaso ya yi magana kan lamarin, ya wallafa a Facebook cewa tsohon gwamnan na yi wa Tinubu aiki ta karkashin ƙasa, maimakon ya hade da tafiyar adawa domin kifar da gwamnatin APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan Kwankwasiyya sun caccaki malamin jami’a
Ƴan Kwankwasiyya sun fusata da Usman Isiyaku, wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu tallata Atiku Abubakar a zaɓen 2023, saboda zargin Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki. Cikin waɗanda suka caccake shi a shafin Facebook, har da Dr. Ibrahim Musa, likitan Gwamna Abba Kabir Yusuf, inda ya zargi malamin da rashin alkibla. Ibrahim Musa ya bayyana cewa binciken da malamin jami’ar ya yi kan Kwankwaso ba gaskiya ba ne, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne.
An gargaɗi magoya bayan Atiku Abubakar
Ɗaya daga cikin manyan magoya bayan na Kwankwasiyya, Dr. Ibrahim Musa, ya ce masoyan Atiku Abubakar na son dora alhakin rashin nasarar ubangidansu a kan Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya ce:
“Suna zargin Kwankwaso da alhakin rashin nasarar ɗan takararsu, sai ka ce Kwankwaso ne ya umarci gwamnonin PDP da Wike ke jagoranta su bar ɗan takararsu.”
A karshe dai bayan an yi masa ca a shafin nasa, Dr. Isiyaku ya bayyana cewa bincike ya ke yi game da Kwankwasiyya da 2027.
Sai dai wasu su na ganin akwai alamar tambaya game da maganar da tsohon malamin na jami'ar Ahmadu Bello Zariya ya yi.
Kwankwaso zai koma APC?
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan cewa Kwankwaso na yi wa APC aiki, Shugaban NNPP a Kano, Hashimu Dungurawa, ya bayyana dalilin da ya hana Kwankwaso shiga kawancen jam’iyyu.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da Legit Hausa, Dungurawa ya ce:
"To yanzu kina da tabbas din ba shi ya haɗa wanna kitimurmurar ba ma? A hada kan mutane a wahalar da ƙwaƙwalwarsu don ya samu ya wuce? Ai wannan abin ki manta da su. Magana ce ta son zuciya..”
Ya ƙara da cewa NNPP za ta firgita sauran jam’iyyu a shirinta na tunkarar zaɓen 2027 nan gaba kaɗan.
Jam'iyyar NNPP ta dura kan Tinubu
A baya, kun samu labarin cewa jam’iyyar hamayya ta NNPP ta yi kakkausar suka ga matakin da shugaba Bola Tinubu ya ɗauka na kakaba dokar ta-ɓaci a jihar Ribas.
Mai magana da yawun NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya ce babu wurin da dokar Najeriya ta ba shugaban ƙasa ikon dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da 'yan majalisa.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa shugaban ƙasa, Tinubu ya ƙware wajen tsallake tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya wajen aiwatar da abin da ya ga dama.
Asali: Legit.ng