'Tsofaffin Ministoci da Sanatoci Sun Shiga SDP don Kifar da Tinubu a 2027,' Gabam
- Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya ce manyan jiga-jigan ‘yan siyasa daga sassan Najeriya na sauya sheka zuwa SDP
- Gabam ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, na daga cikin fitattun ‘yan siyasan da suka koma jam’iyyar daga APC
- A cewarsa, sama da manyan mutane 300, ciki har da tsofaffin ministoci da sanatoci, sun sauya sheka don shiga tafiyar SDP a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Gabam, ya ce jam’iyyarsu na karɓar ‘yan siyasa daga dukkan jihohin Najeriya domin ƙarfafa jam’iyyar gab da babban zaɓen 2027.
A cewarsa, kowace rana akwai sababbin mutane da ke sauya sheka zuwa SDP, ciki har da manyan ‘yan siyasa da suka riƙe muƙamai daban-daban a gwamnatin Najeriya.

Asali: Twitter
Shehu Musa Gabam ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin shiyasa na Channels TV, inda ya jaddada cewa burinsu shi ne kwace mulki daga APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manyan ‘yan siyasa na shiga SDP - Gabam
Shehu Musa Gabam ya bayyana cewa jam’iyyar SDP na ci gaba da samun karɓuwa daga manyan ‘yan siyasa da suka fito daga jam’iyyun APC da PDP.
Ya ce tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shiga SDP, kuma akwai sauran jiga-jigan siyasa da za su biyo sahu a makwanni masu zuwa.
A cewarsa, idan aka duba bayanai da suka tattara, sama da mutum 300 sun fita daga tafiyar su ta baya domin shiga SDP, ciki har da tsofaffin ministoci da sanatoci.
SDP na shirin karɓar mulki daga hannun APC
Shehu Gabam ya ce burinsu na siyasa shi ne karɓar mulki daga APC a zaɓen 2027, domin ceto al’ummar Najeriya daga halin da take ciki.
Ya bayyana cewa kowace jam’iyya ta na da burin karɓar mulki, PDP na kokarin komawa kan karagar mulki, yayin da APC ke son ci gaba da rike shi, amma SDP za ta kawo sabon salo.
Ya ce rashin sauraron koke-koken jama’a na iya jawo wa APC faduwa a zaɓen gaba, saboda hakan na nuna gazawarta a shugabanci.

Asali: Facebook
Gabam ya ce APC na iya faduwa a 2027
Shugaban SDP ya ce kwarewar siyasar Bola Tinubu ba ita ce kadai za ta ba APC damar lashe zaɓe a 2027 ba.
A cewarsa:
“Idan akwai ƙwarewa da dabarun siyasa, ba za a samu kura-kuran da ake yi a yau ba. Duk wanda bai yi daidai ba, za a iya kawar da shi a zaɓe.”
Ya ce Najeriya na da dimbin mutane masu basira da za su iya jagoranci, don haka babu wani mutum guda da ya mallaki ilimin shugabanci fiye da kowa.
Binani ta gana da shugaban jam'iyyar SDP
A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar 'yar takarar gwamna a jam'iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta gana da shugaban SDP na kasa.
Shugaban jam'iyyar, Shehu Musa Gabam ya ce sun tattauna lamura da suka shafi siyasar Najeriya da ci gaban kasa yayin ganawar da suka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng