Abin da Hukumar INEC Ta Yi kan Shirin Yi Wa Natasha Kiranye daga Majalisa
- Hukumar INEC ta gudanar da taro kan shirin kiranye ga Natasha Akpoti-Uduaghan, bayan fiye da masu zabe 250,000 sun sa hannu kan bukatar
- Akpoti-Uduaghan ta musanta cewa ta nemi gafara daga shugabancin majalisa, ta ce tana nan kan matsayinta cewa Godswill Akpabio ya yi mata cin zarafi
- 'Yar siyasar da ta yi fice ta ce bata taba janye kalamanta ba, kuma ba za ta yi shiru ba, tana zargin ana kokarin bata mata suna da yada karya
- Duk wannan na zuwa ne bayan zargin da Sanata Natasha ta yi kan shugaban majalisa, Godswill Akpabio da nemanta da lalata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
FCT, Abuja - Shugabannin Hukumar INEC sun gudanar da taro kan korar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga kujerarta.
Hukumar ta dauki matakin ne bayan wasu ƴan mazabarta na shirin yi mata kiranye daga Majalisar Dattawa.

Asali: Facebook
Yadda ake shirin yi wa Natasha kiranye a Kogi

Kara karanta wannan
Daga karshe Sanata Natasha ta nemi afuwar majalisar dattawa? Ta fito ta fede gaskiya
Thisday ta ruwaito cewa shugabannin hukumar INEC sun yi ganawar a jiya Litinin 24 ga watan Maris, 2025 bayan karɓar korafi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jiya Litinin, magoya bayanta suka mamaye hedikwatar INEC a Abuja, suna bukatar a tsige ta.
Daga bisani, a jiya Litinin din, hukumar INEC ta tabbatar da cewa ta yi taro don tattauna bukatar tsige sanatar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Sanarwar ta ce:
“Mun shiga taro kan batun tsige Sanata Natasha."

Asali: Twitter
Kogi: Mazabar Natasha sun taso ta a gaba
Wasu daga cikin mutanen yankinta sun kai wa INEC bukata da ke cewa sun rasa amana a gare ta kuma suna so a tsige ta.
A cewarsu:
“Mu ‘yan yankin Kogi ta Tsakiya, mun yanke shawarar amfani da ‘yancinmu na kundin tsarin mulki don neman tsige Sanata Akpoti-Uduaghan.”
“Bukatar korar ta na bisa sashe na 68 na kundin tsarin mulkin 1999, da kuma dokokin INEC kan korar ‘yan majalisa.”
Ƴan mazabar suka ce sun rasa amana daga gare Sanata Natasha saboda zarge-zargen cin hanci da kuma almundahana da rashin bin doka da bata sunan yankin a idon duniya.
Sun kara da cewa:
“Sanatar ta samu kujerarta ne bayan hukuncin kotun daukaka kara a ranar 31 ga Oktoba, 2023, wanda ya tabbatar da PDP a matsayin mai nasara.”
“Mu na bukatar korar ta saboda mun rasa amana a gare ta kan almundahana, cin hanci, da rashin bin doka, wanda ya bata sunan yankinmu.”
“Mu na tabbatar da cewa fiye da rabin masu zabe sun rattaba hannu a kan bukatar, don haka muna bukatar INEC ta dauki mataki nan take.”
- Cewar majiyar
Shugaban masu neman tsige ta, Omole Charity, ta ce su ne suka zabe ta, kuma yanzu sun yanke shawarar korarta daga kujerarta na Sanata, cewar Punch.
Natasha ta musanta ba majalisa hakuri
Kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta musanta rahoton cewa ta nemi gafarar majalisa, ta na mai cewa hakan karya ne kuma ba za ta janye maganarta ba.
Ta zargi wasu mutane da kokarin juya hankalin jama’a da labaran karya, ta na mai cewa dole jama’a su yi watsi da wadannan rahotanni.
Hakan ya biyo bayan zargin da take yi wa shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio da cewa ya neme ta da lalata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng