2027: 'Yar Takarar Gwamnan APC, Aisha Binani ta Gana da Shugaban SDP

2027: 'Yar Takarar Gwamnan APC, Aisha Binani ta Gana da Shugaban SDP

  • Shugaban SDP, Shehu Musa Gabam, ya kai ziyarar girmamawa ga Sanata Aishatu Dahiru Ahmed (Binani) saboda watan Ramadan
  • Sun tattauna kan makomar Najeriya da rawar da mata ke takawa a siyasa domin tabbatar da mulkin adalci da ci gaban kasa
  • Mutane da dama sun jinjinawa tattaunawar, su na masu bayyana Sanata Binani a matsayin shugaba mai kishin kasa da hangen nesa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - A cikin watan Ramadan mai albarka da muke ciki, shugabannin siyasa da dama na amfani da damar don tattaunawa kan makomar Najeriya.

Shugaban SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya kai ziyara ga Sanata Aishatu Dahiru Ahmed (Binani), wacce ake yi wa kallon daya daga cikin manyan matan siyasa masu kishin kasa.

Kara karanta wannan

'Muna bayan Wazirin Adamawa': Matasa sun dauko tafiyar kifar da Tinubu a 2027

Binani
Shugaban SDP na kasa ya ziyarci Aishatu Binani. Hoto: Shehu Musa Gabam, SDP National Chairman
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Shehu Musa Gabam ya yi bayan ziyarar a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aishatu Binani ta rike manyan mukamai a Najeriya, ciki har da minista da sauransu. Kuma ta yi takarar gwamna a APC a jihar Adamawa.

Shugaban jam'iyyar SDP ya ziyarci Binani

Shugaban jam’iyyar SDP, Shehu Musa Gabam, ya bayyana ziyarar da ya kai wa Sanata Binani a matsayin wata dama ta musayar ra’ayi kan makomar Najeriya.

A cewarsa, Sanata Binani shugaba ce mai kishin kasa, wacce ke ba mata da matasa kwarin gwiwa don su shiga harkar siyasa da shugabanci.

Ya ce tattaunawar su ta mayar da hankali kan mulkin adalci da yadda ake bukatar sauyi mai amfani a siyasar Najeriya.

Gabam ya kuma jaddada cewa jam’iyyar SDP ce matattarar ingantaccen shugabanci, kuma ya bukaci matasa da mata su rungumi tafiyar don gina kasa mai kyakkyawar makoma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware 'yan APC a jiha 1, ya ba su buhunan shinkafa 7,000 saboda Ramadan

Martanin jama'a kan haduwar Binani da SDP

Mutane sun yi martani bayan ziyarar a shafin sada zumunta na Facebook, inda da dama suka yaba da kokarin shugabannin biyu.

A karkashin rubutun da Gabam ya yi, Onimisi Nasirudeen, ya ce:

"Gwagwarmayar ku ta ganin an samu mulkin adalci da damawa da kowa abin a yaba ne. Najeriya na bukatar shugabanni masu gaskiya kamar ku."

Haka kuma, wani mai suna Mallam Adamu Masun Bashar, ya ce:

"Muna ci gaba da goyon bayan gwagwarmaya don tabbatar da adalci ga kowa a Najeriya."

Shi ma M Usman Geidam ya jinjinawa ziyarar, yana mai cewa:

"Sanata Binani shugaba ce mai hangen nesa, kuma irin wannan tattaunawa ce za ta kawo sauyi a kasa."
Aisha Binani
Binani da ta yi takarar gwamna a jihar Adamawa karkashin APC. Hoto: Aisha Dahiru Binani
Asali: Facebook

Shawarar Gabam ga mata da matasa

Shehu Musa Gabam ya bukaci mata da matasa su shiga harkokin siyasa domin tabbatar da mulkin gaskiya.

Kara karanta wannan

Barau na kara barazana ga Abba a Kano, 'yan fim din Dadinkowa sun goyi bayansa

Ya ce lokaci ya yi da za a hada kai domin kawo ci gaba, yana mai kira da a mara wa jam’iyyar SDP baya don gina Najeriya mai inganci.

A cewarsa:

"Mu hadu mu gina Najeriya mai inganci tare!"

'Yan adawa na shirin haduwa a Najeriya

A wani rahoton, kuj ji cewa shugabannin adawa a Najeriya sun fara shirin hadaka da domin tunkarar APC a zaben 2027.

A wani taro da suka yi a Abuja a makon da ya wuce, Atiku Abubakar ya bayyana cewa akwai shiri na musamman domin hada kan 'yan adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng