'Muna bayan Wazirin Adamawa': Matasa Sun Ɗauko Tafiyar Kifar da Tinubu a 2027

'Muna bayan Wazirin Adamawa': Matasa Sun Ɗauko Tafiyar Kifar da Tinubu a 2027

  • Kungiyar matasa ta AYW ta bayyana Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da za ta marawa baya a zaben shugaban kasa na 2027
  • Matasan kungiyar sun ce Atiku na da kwarewa a mulki, kasuwanci, da diflomasiyya, wanda ya sa ya fi dacewa da shugabanci
  • Shugaban AYW, Odih Rowland ya ce Atiku mutum ne da zai hada kan kasa, ya inganta tattalin arziki, da kawo ci gaba ga ‘yan Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Yayin da babban zaben 2027 ke karatowa, kungiyar matasa ta Atiku Youth Wing (AYW) ta bayyana Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar da ta fi so.

Shugaban kungiyar, Odih Rowland, ya ce sun yarda cewa Atiku na da hazaka, hangen nesa, da jajircewar da zai kawo ci gaba mai ma’ana a kasar.

Kara karanta wannan

2027: 'Yar takarar gwamnan APC, Aishatu Binani ta gana da shugaban SDP

Matasa sun magantu da suka ayyana Atiku Abubakar a matsayin dan takararsu na 2027
Matasa sun goyi bayan Atiku yayin da ake tunkarar zaben 2027. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

Zaben 2027: Matasa sun goyi bayan Atiku

A cewar kungiyar, Atiku na da kwarewa a fannin mulki, kasuwanci, da diflomasiyya, wanda ya sanya shi zama mafi dacewa da shugabancin Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan AYW sun ce Atiku na da cikakken kudirin ganin al’ummar kasar nan sun samu ci gaba da walwala, kuma hangen nesansa ya dace da makomar Najeriya.

"Yayin da muke gab da shiga babban zaben 2027, muna bukatar zaben shugaban da ya fahimci matsalolinmu, kuma mai hangen nesan da zai kawo sauyi mai ma’ana.
"Wannan shugaba shi ne Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007.

- Inji Odih Rowland.

Matasa sun gwarzanta Atiku Abubakar

Matasan AYW sun bayyana Atiku a matsayin gogaggen shugaba da ya jagoranci shirye-shirye a fannoni daban-daban lokacin da ya ke kan mulki.

Kungiyar ta ce:

"Nasarorinsa a matsayin mataimakin shugaban kasa, musamman rawar da ya taka a kwamitin kasa na zamanantar da hukumomi (NCP), sun haifar da ci gaba ga tattalin arzikin Najeriya

Kara karanta wannan

Gudaji Kazaure: Babban jigo a APC ya gana da Atiku, ya fadi shirin kifar da Tinubu

Kungiyar ta ce Atiku ya na da kishin Najeriya, wanda ake iya ganin haka karara a ayyukansa na tallafa wa ilimi, kiwon lafiya, da inganta rayuwar matasa.

"Goyon bayansa ga matasa da 'yan Najeriya marasa galihu shaida ce ta kyawawan halayensa da kyakkyawan salon shugabancinsa," inji kungiyar.

Ana so 'yan Najeriya su goyi bayan Atiku

Atiku Abubakar ya samu goyon bayan matasa gabanin zaben 2027
Gabanin zaben 2027, matasa sun nuna goyon bayansu ga Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Kungiyar ta jaddada cewa Atiku mutum ne da zai hada kan al’umma, kuma zai iya kawo hadin kai tsakanin kabilu, addinai, da yankuna daban-daban.

Jaridar Leadership ta rahoto matasan sun bukaci ‘yan Najeriya da su duba cancanta da kwarewar Atiku Abubakar wajen ciyar da kasa gaba.

"Mu hade wuri guda domin mara wa shugaba (Atiku) baya wanda yake da burin cigaban kasar mu," in ji kungiyar.

Atiku Youth Wing ta bukaci ‘yan kasa su marawa Atiku baya a matsayin zabi mafi dacewa domin cire Najeriya daga matsin da take ciki a yanzu.

Gudaji Kazaure ya kama layin Atiku Abubakar

Kara karanta wannan

2027: Ta fara tsami tsakanin ƴan adawa, burin Atiku da maganar yanki na son ta da kura

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Atiku Abubakar ya karɓi baƙuncin Hon. Gudaji Kazaure, inda suka tattauna kan yanayin Najeriya da shirin fuskantar zaɓen 2027.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan haɗin gwiwar ‘yan siyasa don ceto Najeriya, tare da samar da shugabanci nagari da zai inganta rayuwar 'yan kasa.

Gudaji Kazaure ya bayyana aniyarsu ta bin tsarin Atiku da shugabannin Arewa domin samar da ci gaba mai dorewa, musamman fitar da Najeriya daga halin da take ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.