Dawowar Fubara: Ana Rade Radin yin Sulhu a Rivers, Wike Ya Yi Magana
- Gwamnonin yankin Kudu maso Kudu da 'yan majalisar tarayya na kokarin kawo karshen rikicin siyasa a Jihar Ribas
- Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da Gwamnatin Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar
- Majalisar wakilai ta kasa na shirin kafa kwamiti don kula da harkokin majalisar dokokin jihar Ribas har sai an samu maslaha
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa shugabannin siyasa daga yankin Kudu maso Kudu, musamman gwamnonin yankin, na kokarin sasanta rikicin Ribas.
Rikicin siyasar jihar Ribas da ke tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara da ‘yan majalisar dokokin Jihar Ribas ya jawo sanya dokar ta-baci.

Asali: Facebook
Shugaban kasa ya yi waje da gwamnatin Fubara
Punch ta wallafa cewa ministan Abuja, Nyesom Wike da ake gani yana da hannu a rikicin ya ce ba ya adawa da matakin sulhu da za a dauka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 18 ga watan Maris, Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Ribas, wanda ya haifar da rudani a harkokin mulki.
Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar, sannan ya nada tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Ibok-Ette Ibas shugaban riko.
Kokarin sasanta rikicin siyasar jihar Ribas
Wasu manyan jiga-jigan 'yan siyasa na ganin cewa dakatar da gwamnan da majalisar dokokin ba shine mafita ba, domin hakan na iya haddasa kama karya a siyasar kasar.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa manufar dokar ta-baci ita ce ba wa bangarorin biyu damar samun lokaci don rage zafin rikicin da kuma shiryawa zaman sulhu.
Haka kuma, an bayyana cewa gwamnonin Kudu maso Kudu da wasu sanatoci na kokarin ganin an cimma maslaha tsakanin bangarorin domin kawo karshen rikicin siyasar Ribas.

Kara karanta wannan
Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna
Majalisar wakilai na shirin kafa kwamiti
Majalisar wakilai ta kasa ta bayyana cewa za ta fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba kan kafa kwamiti da zai rike ragamar harkokin majalisar dokokin jihar Ribas.
Mataimakin mai magana da yawun majalisar, Philip Agbese, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da shi a Abuja, inda ya ce manufarsu ita ce tabbatar da zaman lafiya a jihar.
A cewarsa:
“Shugaban majalisa da sauran shugabanni na aiki kan wannan batu, kuma nan ba da jimawa ba za a fitar da sanarwa kan hukuncin da za a dauka.”

Asali: Facebook
Abin da wike ya fada kan sulhu da Fubara
A daya bangaren kuma, hadimin Ministan Abuja, Lere Olayinka, ya bayyana cewa Nyesom Wike ba ya adawa da duk wani yunkuri na sulhu a Ribas.
Olayinka ya ce:
“Minista ba ya adawa da zaman sulhu ko tattaunawa. A baya an yi kokarin sasanta rikicin amma wasu suka soki shugaba Tinubu da cewa ba shi da hurumin shiga cikin rikicin.”
Tun bayan nasarar Fubara a 2023, dangantakarsa da Wike ta tabarbare, lamarin da wasu ke gani shine tushen rikicin siyasar da ake fama da shi a jihar Ribas.
Shugaban riko na kan aikinsa
Shugaban riko na jihar Ribas, Ibok-Ette Ibas, ya fara gudanar da ayyukansa, inda ya bukaci bangarorin da ke rikici su rungumi zaman lafiya da hadin kai.
Yayin da ya karbi ragamar mulki, ya yi alkawarin yin aiki tare da shugabanni da ‘yan siyasa domin daidaita rikicin da ya addabi jihar.
A gefe guda, gwamnonin yankin Kudu maso Kudu sun gudanar da taro don tattauna hanyoyin warware matsalar.
Daga cikin abubuwan da suka tattauna har da bukatar shugaban kasa ya sake duba matakin da aka dauka kan gwamnatin Fubara.
Wasu daga cikinsu na ganin cewa dole ne a samu matsaya da za ta gamsar da dukkan bangarorin da ke rikici.
Hakazalika, wasu sanatoci da suka fito daga yankin sun nuna damuwa kan yadda rikicin ke kara dagulewa. Sun bukaci majalisar tarayya da ta yi gaggawar kafa kwamitin da zai kula da majalisar dokokin jihar Ribas.
Martanin gwamnoni kan dakatar da Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun yi magana kan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya yi.
Kungiyar gwamnoni ta NGF ta ce ta zabi yin shiru ne a kan rikicin Ribas saboda tsoron faruwar sabani a tsakaninsu kamar yadda aka samu a baya.
Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan ta hanyar kara bayani kan shugaban riko na Rivers
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng