Ribas: Tambuwal Ya Tona Yadda aka Yi Watsi da Doka a Majalisa don Biyan Buƙatar Tinubu

Ribas: Tambuwal Ya Tona Yadda aka Yi Watsi da Doka a Majalisa don Biyan Buƙatar Tinubu

  • Tsohon Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya soki matakin shugaba Bola Tinubu na sa dokar ta ɓaci a Ribas
  • Ya ce ba a bi tanadin kundin tsarin mulki ba, domin ba a samu amincewar kason 'yan majalisa da zai ba da damar tabbatar da dokar
  • Sanatan ya kara da bayyana yadda tsofaffin shugabanni, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan su ka sa dokar ta ɓaci a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers – Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah wadai da kakaba dokar ta ɓaci a jihar Ribas da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a Ribas tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da majalisar dokokin jihar na tsawon watanni shida.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi lokacin da Tinubu zai janye dokar ta baci a Ribas

Tambuwal
Tambuwal ya yi fatali da dokar ta baci a Ribas Hoto: The Senate President/Aminu Waziri Tambuwal Media
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa haka kuma, ya naɗa tsohon babban jami’in rundunar sojin ruwa, Ibok-Ete Ibas, a matsayin shugaban riko a jihar, lamarin da ya fusata 'yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tambuwal ya yi tir da dokar ta ɓaci a Ribas

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Tambuwal, wanda tsohon shugaban majalisar wakilai ne, ya bayyana cewa sanya dokar ta ɓaci ya saba da tanadin kundin tsarin mulki ba.

Ya ce majalisar dattawa ba ta samu kaso biyu bisa uku na yawan 'yan majalisa da ake bukata don amincewa da bukatar Shugaban kasa, Bola Tinubu ba.

Tambuwal ya ce:

"Abin da doka ta tanada shi ne dole ne a samu kaso biyu bisa uku na dukkanin 'yan majalisa domin amincewa da kudurin. Ba kawai wadanda suka halarci zaman kadai ba."

"Tinubu ya rasa goyon baya kan Ribas," Tambuwal

Sanatan da ke wakiltar Sokoto ta Kudu ya bayyana cewa babu tabbacin Sanatacin da su ka halarci zaman majalisar a ranar tabbatar da dokar a baci sun kai 72 zuwa 73.

Kara karanta wannan

"Me yasa ba ka sa a Legas ba?" An tunkari Tinubu da tambaya kan dokar ta ɓaci

Ya ce ya na da tabbacin biyu bisa uku na Sanatocin ba su halarci zaman da aka yi don tabbatar da dokar ta ɓaci a jihar Ribas ba.

Majalisa
Tambuwal ya ce 'yan majalisa da dama ba su halarci zaman sa dokar ta baci a Ribas ba Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Tambuwal ya ce:

"Idan ka kwatanta hakan da abin da kundin tsarin mulki ya tanada – wanda ke buƙatar kaso biyu bisa uku na duka 'yan majalisar dattawa don amincewa da dokar ta ɓaci – za ka fahimci cewa abin da aka yi bai dace da dokar kasa ba."

Tsohon kakakin majalisar ya kara da cewa dole ne majalisa ta yi aiki ne da tsarin mulki, dokokinta da kuma yadda aka saba gudanar ayyuka bisa doka.

Ribas: Tambuwal ya yi bayanin dokar ta ɓaci

Tambuwal ya kuma tuna yadda majalisar tarayya ta nemi kaso biyu bisa uku na 'ya'yanta kafin a ayyana dokar ta ɓaci a jihohin Filato, Borno, Adamawa da Yobe a zamanin shugabannin kasa Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Kara karanta wannan

Dokar ta baci a Ribas: Ana zargin Shugaba Tinubu da 'juyin mulki'

Sanatan ya ce:

"A zamanin shugaba Obasanjo, sai da aka nemi kashi biyu bisa uku a majalisar dattawa da ta wakilai kafin a ayyana dokar ta ɓaci."
"A shekarar 2013, lokacin da Jonathan ke mulki, an ayyana dokar ta ɓaci a Borno, Adamawa da Yobe, sai da muka samu kaso biyu bisa uku kafin hakan ya tabbata."
"To, me ya hana wannan majalisa ta yanzu yin la’akari da irin wannan tsari da aka saba bi?"

Ribas: An zargi Akpabio da murkushe adawa

A baya, kun samu labarin cewa Sanata Seriake Dickson, mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a PDP, ya zargi shugaban majalisa, Godswill Akpabio da dakile masu adawa da dokar ta ɓaci a Ribas.

A yayin zaman majalisar dattawa domin neman amincewarsu kan dokar, Sanata Dickson da wasu Sanataci sun fice daga zauren majalisar kafin a amince da kudurin dokar ta ɓaci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng