2027: Ta Fara Tsami Tsakanin Ƴan Adawa, Burin Atiku da Maganar Yanki na Son Ta da Kura

2027: Ta Fara Tsami Tsakanin Ƴan Adawa, Burin Atiku da Maganar Yanki na Son Ta da Kura

  • Yunkurin kafa kawancen jam’iyyun adawa domin fuskantar Tinubu a 2027 na fuskantar cikas saboda takarar Atiku da batun karba-karba a mulki
  • Jiga-jigan siyasa daga Kudu suna goyon bayan ci gaba da mulki daga yankin na tsawon shekaru takwas, wanda ke kara rikita lamarin
  • Peter Obi da abokan kawancensa na son a bar Kudu ta kammala wa’adin mulki, ammawasu na kin amincewa da tsarin yanki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yayin da kokarin kafa kawance don kalubalantar Shugaba Tinubu a 2027 ke kara karfi, an fara samun matsaloli.

Rahotanni sun ce burin Atiku Abubakar da batun yanki na jinkirta tattaunawar jagororin siyasa kan zaɓen 2027.

Ana ci gaba da hasashen rigima kan hadakar jam'iyyun adawa
Wasu matsaloli sun fara shiga cikin shirin haɗaka kan zaben 2027. Hoto: Peter Obi, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai.
Asali: UGC

Yadda ƴan adawa ke shiri kan zaben 2027

Wata majiya mai tushe ta fadawa Punch cewa ɓangaren Peter Obi da Rotimi Amaechi na bukatar mulki ya ci gaba daga Kudu na tsawon shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Nasarori 3 da Nyesom Wike ya samu a cikin kwanaki 3 a siyasar jam'iyyar PDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta kara da cewa, jinkirin ya biyo bayan rashin tabbacin ko Atiku zai sake tsayawa takara ko sabanin haka a 2027.

Ta ce 'yan siyasa daga Kudu na jin tsoro su shiga cikin shirin don ka da hakan ya bata musu dama da yankinsu a gaba.

Bayan ficewar El-Rufai daga APC zuwa SDP a ranar 10 ga Maris, tattaunawar ta kara karfi.

Atiku da wasu ‘yan adawa sun ce taron da suka yi a ranar Alhamis shi ne kaddamar da wannan sabuwar kawance.

Ya ce:

“Eh, wannan shi ne shirin kawance na ‘yan adawa kafin 2027.”
Ana ci gaba da tattaunawa kan hadakar jam'iyyun adawa saboda zaben 2027
Wasu majiyoyi sun ce an fara samun matsaloli kan shirin hadaka saboda zaben 2027. Hoto: People's Democratic Party, PDP.
Asali: UGC

Manyan jiga-jigan APC da suka halarci taron

Taron ya samu halartar tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da Peter Ahmeh na CUPP da Segun Showunmi.

Wasu daga cikin wadanda aka ambata amma ba su halarta ba su hada da Rotimi Amaechi, Kayode Fayemi da Abdullahi Adamu.

Majiyoyi sun bayyana cewa jinkirin tattaunawa ya faru ne saboda yawancin masu ruwa da tsaki na da burin tsayawa takara a 2027.

Kara karanta wannan

"Ba za ku tabuka komai ba," Ministan Tinubu ya yi watsi da kwancen adawa

“Obi da Amaechi na da niyyar maye gurbin Tinubu, don haka suna son mulki ya ci gaba daga Kudu.”
“Sannan Atiku na kokarin samun dama ta karshe don tsayawa takara a 2027, masu ruwa da tsaki daga Kudu na tsoron shiga tattaunawa ba tare da sanin matsayin Atiku ba.”

- Cewar majiyar

Peter Ahmeh na CUPP, wanda ke kusa da Obi, ya tabbatar da cewa dole ne dan Kudu ya tsaya takara a 2027.

A hirarsa da Sunday PUNCH, Ahmeh ya ce dan Kudu na da karfin kayar da Tinubu a zabe.

Ya ce:

“Ba za mu wofantar da yarjejeniyar karba-karba tsakanin Arewa da Kudu ba, a matsayina na dan Arewa, na yarda cewa mulki ya rika zagayawa tsakanin yankuna biyu.”
“Yarjejeniyar shekaru takwas-takwas tana da amfani, koda yake dole ne ayi zabe kuma ‘yan Najeriya su yanke.”

Dalung ya gargadi Tinubu kan salon mulkinsa

Kun ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya gargadi Bola Tinubu da ya gyara tafiyarsa saboda zaben 2027.

Dalung ya ce bai san ko Bola Tinubu zai ci ko zai fadi ba a 2027, amma 'yan Najeriya sun fara fusata matuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel