Ministan Buhari Ya Hango Faduwar Tinubu a 2027, Ya Kwatanta hakan da Lamarin Jonathan

Ministan Buhari Ya Hango Faduwar Tinubu a 2027, Ya Kwatanta hakan da Lamarin Jonathan

  • Tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya ce bai san ko Bola Tinubu zai ci ko zai fadi ba a 2027, amma 'yan Najeriya sun fara fusata matuka
  • Dalung ya bayyana cewa shugabanni da suka gabata sun kashe kudi fiye da Tinubu, amma hakan bai hana su faduwa ba saboda gazawarsu
  • Ya kwatanta halin da ake ciki da lokacin da Jonathan ya fadi, yana cewa irin wannan guguwa na sake kunno kai a kasar nan
  • Dalung ya shawarci Tinubu da ya yi shugabanci da amana, ya tuna cewa Najeriya kasa ce mai kabilu da harsuna masu tarin yawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung ya yi magana kan siyasar Bola Tinubu a zaben 2027.

Dalung ya ce akwai alamu Tinubu ka iya samun matsala duba da yadda yake gudanar da mulkinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 35 sun yi matsaya kan dakatar da Fubara da Tinubu ya yi

Tsohon minista ya yi hasashen abin da da zai faru da Tinubu a 2027
Solomon Dalung ya ce Tinubu zai iya fuskantar matsala irin na Jonathan a 2015. Hoto: @aonanuga1956.
Asali: Twitter

Dalung ya magantu kan zaben Tinubu a 2027

Dalung ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da jaridar Punch a jiya Asabar 22 ga watan Maris din shekarar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce ba zai iya sanin ko Tinubu zai fadi a zaben 2027 ba amma ya san halin ƴan Najeriya.

Tsohon ministan ya ce:

"Ba zan iya cewa ko zai ci ko zai fadi ba, amma na san cewa 'yan Najeriya sun riga sun koyar da shugabanni darasi.
"Wadanda aka koyar da darasin ma ba su da muni irin wanda Tinubu ke nuna wajen tafiyar da kasa.
"Wadancan shugabannin sun kashe kudi fiye da Tinubu, amma hakan bai ceto su ba, duk da haka, basu samu nasara ba."
Tsohon minista ya soki salon mulkin Bola Tinubu
Solomon Dalung ya shawarci Tinubu kan kawo sauyi a kasa kafin lokaci ya kure. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Goodluck Jonathan.
Asali: Facebook

2027: Dalung ya yi hasashen zaben Tinubu

Dalung ya ce akwai alamun guguwar siyasa da ta yi sanadin Goodluck Jonathan a mulki ita za ta kawo karshen mulkin Tinubu duba da yadda yake tafiyar da ita.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi martani kan haduwar Atiku, El Rufa'i da Obi don kifar da Tinubu a 2027

Ya shawarci Tinubu da ya yi abin da ya dace domin kawo karshen matsalolin da ke kasar wurin gudanar da shugabanci yadda ya kamata.

"Ina ganin irin guguwar da ta kifar da Jonathan tana dawowa, amma ban san yadda za ta kare ba tukuna.
"Duk da haka, ina ganin lokaci ya yi da shugaban kasa zai gargadi kansa, ya rika gudanar da mulki a matsayin shugaban Najeriya.
Najeriya na da kabilu sama da 538 da harsuna sama da 1000, wani irin shugaba ne zai raina irin wannan kasa?"

Tsohon ministan ya ce kasar nan na da mafi yawan masu hankali a duniya, Tinubu ba zai fi kowa wayo ba, ya kamata ya mutunta amana.

Dalung ya zargi mugaye a gwamnatin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa tsohon minista a Najeriya, Solomon Dalung ya bayyana cewa 'yan-ba-ni-na-iya da ke kusa da shugaba Bola Tinubu sun yi yawa.

Kara karanta wannan

"Ka da a ɗora mun laifi": Gwamna Fubara ya cire tsoro, ya ƙaryata kalaman Tinubu

Dalung ya ce irin wadannan mutane sun fi na mulkin Muhammadu Buhari karfi da hatsari wurin juya akalar gwamnati.

Solomon Dalung ya bayyana cewa mutanen za su iya yin illa ga mulkin Bola Tinubu tare da jefa ‘yan Najeriya cikin damuwa da talauci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng